Masu gwaji sun kamu da cutar covid-19 a Kano

Masu gwaji sun kamu da cutar covid-19 a Kano

- Jigon kwamiti na musamman a kan coronavirus da gwamnatin tarayya ta kafa, Dr Aliyu Sani, ya bayyana cewa masu yin gwajin cutar a Kano sun kamu

- Dr Sani ya ce hakan ne ma babban dalilinsu na rufe dakin gwajin cutar

- Game da yawan mace-macen mutane da aka samu a birnin Kano, babban likitan ya ce suna ci gaba da bincike domin gano makusudin mace-macen

Babban jigon kwamiti na musamman a kan coronavirus da gwamnatin tarayya ta kafa, Dr Aliyu Sani, ya bayyana cewa masu yin gwajin annobar ta COVID-19 a Kano sun kamu.

A cewar Dr Sani wannan ne ma babban makusudin da ya sa aka rufe dakin gwajin cutar da ke asibitin Malam Aminu Kano.

Sai dai jigon kwamitin na NCDC bai bayyana yawan adadin mutanen da suka kamu da cutar ba.

Masu gwaji sun kamu da cutar covid-19 a Kano
Masu gwaji sun kamu da cutar covid-19 a Kano
Asali: UGC

A kan kokawar da ma'aikatan cibiyar gwajin ta Kano suka yi cewa rashin kayan aiki ne ya sa aka dakatar da yin gwajin, Dr Sani ya ce:

"Ko a jiya Laraba, 22 ga watan Afrilu mun tura kayan gwaji zuwa Kano", amma ba za su iya amfani da wurin ba saboda akwai bukatar tsaftace wurin.

Hakan baya rasa nasaba da yadda ba a samu ko da mutum daya ba mai dauke da cutar korona a Kano ranar Laraba ba.

A alkaluman da hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta kasar, NCDC ta fitar da daren Larabar babu masu cutar daga jihar Kano.

Kididdiga ta ranar Talata dai ta nuna jihar na da masu dauke da cutar 73.

Dr Aliyu Sani ya ce muna sane da irin halin da jihar Kano take ciki kasancewar idan cutar ta ci gaba da bazuwa a Kano to tamkar gabadaya arewacin Najeriya ya kamu ne.

"Akwai kunshi na musamman da za a bai wa jihar Kano kamar yadda aka bai wa jihar Legas."

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari: Tsoffin yan majalisa sun tsayar da Abba Ali a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari na gaba

Game da yawan mace-macen mutane da aka samu a birnin Kano, Dr Sani ya ce suna ci gaba da bincike domin gano makusudin mace-macen.

Ya ce an kafa kwamitoci daban-daban domin gano cewa ko cutar korona ce ke kisa a Kano ko sankarau ne ko kuma zazzabin Lassa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel