Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59

Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59

An samu mutane 23 a jahar Kano da suka kara kamuwa da annobar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus, wanda hakan ya kawo adadin masu cutar a Kano zuwa 59.

Hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC ce ta sanar da haka a daren Litinin cikin bayanin da ta fitar dangane da halin da ake ciki game da Coronavirus a Najeriya.

KU KARANTA: Batun sauya ma jami’ar jahar Imo suna zuwa jami’ar Abba Kyari karya ne – Gwamna

Cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce an samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar a Najeriya gaba daya, sai dai a wannan karo ba’a samu ko mutum daya ba a jahar Legas.

Sanarwar ta kara da cewa jahar Kano ce kan gaba a jiya inda take da sabbin masu cutar su 23, Gombe na da 5, Kaduna uku, Borno 2, Abia 2, yayin da Abuja, Sokoto da Ekiti suke da 1 kowanne.

“Zuwa karfe 11:10 na daren Litinin, 20 ga watan Afrilu akwai mutane 665 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, inda mutane 22 suka mutu sai 188 da suka warke kuma aka sallamesu.” Inji shi.

Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59

Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59
Source: Facebook

A hannu guda kuma gwamnatin jahar Sakkwato ta sanar da bullar mugunyar cutar Coronavirus a jahar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka da kansa cikin wani jawabi da ya yi ma al’ummar jahar Sakkwato inda ya fara da fadin “Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un”

Ya cigaba da jawabin sa kamar haka: “Jama’an jahar Sakkwato, tare da alhini da damuwa nake sanar da ku cewa annobar COVID-19, ma’an Coronavirus ta shigo jahar Sakkwato. A yanzu haka mun fara shirin killace mutumin a wurin killacewa dake Amanawa.”

Gwamnan ya ce a yanzu haka mutumin dake dauke da cutar ya fara samun kulawa a asibitin koyarwa ta jami’ar Usmanu Danfodiio dake jahar Sakkwato.

“Ina kira ga jama’a su cigaba da bin ka’idojin da aka shimfida don kare yaduwar cutar nan, muna jin sa ne a baya, amma a yanzu ya shigo cikinmu, don haka ya kamata mu zage damtse domin kare yaduwarsa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel