Samaila Isa Funtua ya yi fatali da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya

Samaila Isa Funtua ya yi fatali da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya

Tsohon minista a jamhuriya ta biyu, Alhaji Sama’ila Isah Funtua ya shawarci masu danganta shi da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da su kai kasuwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito an ambaci Funtua mai shekaru 78 daga cikin wadanda ake sa ran zasu maye gurbin marigayi Abba Kyari wanda ya rasu a dalilin cutar COVID-19 a ranar Juma’a.

KU KARANTA: Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga

Funtua, ya taba zama jami’in mulki a Katsina NA tsawon shekaru 7, ministan ruwa, kuma yana cikin mutanen da suka tsara daftarin kundin tsarin mulki a shekarar 1994-1995.

Shi ne mai kamfanin gine gine na Bulet, kamfanin mutum daya mafi girma a Najeriya da ta gina mafi kyawun gine ginen dake babban birnin tarayya Abuja, kuma babban dan jarida ne.

Don haka ya ce baya bukatar wannan mukamin saboda a cewarsa shi kan sa yana daukan mutane aiki a Najeriya, don haka ya girmi wani ya dauke shi aiki a wannan lokaci.

Samaila Isa Funtua ya yi fatali da mukamin ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya
Samaila Isa Funtua ya yi fatali da mukamin ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya
Asali: UGC

“Ni ma ina daukan ma’aikata aiki ne, don haka babu yadda za’ayi a dauke ni aiki. Ni fa minista ne a shekarar 1983, don haka wani mukami zai bani sha’awa yanzu? Na ji kunya da wata jarida ta danganta ni da wannan mukami saboda tsabar jahilci.” Inji shi.

Daga cikin wadanda ake hasashen shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zabo sabon hadimin nasa daga cikinsu akwai gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Sauran sun hada da hadimin shugaban kasa a kan harkoki na musamman, Yau Darazo, shugaban kwastam, Hamid Ali, ministan ilimi, Adama Adamu da kuma Babagana Kingibe.

A hannu gudaa, jama’a sun cigaba da bayyana kyawawan halayen marigayi Abba Kyari wanda wasu ke ganin tamkar shi ne matsalar gwamnatin Buhari, sai ga shi ana ta wanke tas!

Shi da yake mika ta’aziyyar mutuwar Kyari, babban lauya Femi Falana ya nemi ya inganta asibitocin Najeriya da fannin kiwon lafiya a matsayin girmamawa ga marigayi Abba Kyari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel