‘Yan Majalisar dokokin Oyo sun amince da ragin albashi domin yaki da COVID-19

‘Yan Majalisar dokokin Oyo sun amince da ragin albashi domin yaki da COVID-19

Ganin halin da annobar cutar Coronavirus ta jefa tattalin arzikin Duniya, gwamnatocin Najeriya sun fara daukar matakai na musamman domin rage radadin da za a yi fama da shi.

A jihar Oyo, gwamnatin Seyi Makinde ta roki ‘yan majalisar dokoki su hakura da wani kaso daga cikin kudinsu. Wannan zai taimaka wajen ganin jihar ta samu zama da kafafunta.

Jaridar The Tribune ta bayyana cewa ‘yan majalisar Oyo sun cin ma matsaya da gwamnatin Seyi Makinde game da kason da za a rage daga cikin kudin da su ke karba a kowane wata.

Rahotannin sun ce ‘yan majalisar dokokin za su hakura da kashi 30% na kudinsu.

Wannan ragi zai fara tasiri ne daga albashin watan Afrilu har sai zuwa lokacin da abubuwa su ka mike.

Mai magana a madadin majalisar dokokin jihar Oyo, Honarabul Kazeem Olayanju, ya shaida cewa shi da abokan aikinsa sun yi wannan ne domin a iya gudanar da sha’anin gwamnati.

KU KARANTA: Abin da ya hana COVID-19 fitinar kasashen Nahiyar Afrika - WHO

Ya ce: “An rage 30% daga cikin abin da mu ke samu a matsayin gudumuwarmu na yaki da annobar COVID-19. Gwamnan ya kawo wannan shawara, kuma mu ka amince da hakan.”

Gwamna Seyi Makinde ya nunawa ‘yan majalisar jihar cewa gwamnatin tarayya ta rage abin da ta ke ba jihar Oyo da kashi 60% a sakamakon annobar Coronavirus da ake fama da ita.

Bayan haka, gwamna Makinde ya yi irin wannan kira ga sauran masu rike da kujeru da manyan mukaman siyasa da su sadaukar da wani abu daga cikin makudan kudin da su ke samu.

Kazeem Olayanju ya ce hakan zai taimaka wajen ganin gwamnatin Oyo ba ta kai ga rage albashin da ake biyan ma’aikata a daidai lokacin da wannan annoba ta zaunar da jama’a a gida.

Wannan annoba da ake fuskanta ta yi sanadiyyar karya farashin gangar danyen mai a Duniya. A dalilin haka Najeriya wanda ta dogara da mai ta yi wa kasafin kudin 2020 garambawul.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: