Gwamna Badaru ya kulle karamar hukumar Kazaure bayan bullar annobar covid-19

Gwamna Badaru ya kulle karamar hukumar Kazaure bayan bullar annobar covid-19

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da kulle karamar hukumar Kazaure bayan tabbatar da samun bullar annobar cutar covid-19 a karamar hukumar, a ranar Lahadi.

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ne ya bayar da umarnin kulle karamar hukumar da yammacin ranar Lahadi.

A cikin sanarwar, wacce aka wallafa a shafin sada zumunta (facebook) na gwamnatin jihar jigawa, an bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga karfe 12:00 na safiyar ranar Litinin.

Sai dai, a cikin sanarwar, babu wani bayani a kan wanda aka tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar covid-19 a karamar hukumar.

Wannan shine karo na farko da aka sanar da cewa wani mazaunin jihar Jigawa ya kamu da kwayar cutar covid-19.

Sannan shine karo na farko da gwamnatin jihar ta sanar da kulle wani gari, ba shiga, ba fita, tun bayan sanar da dokar nesanta da hana taro da rufe ma'aikatun gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel