An hana wasu hadiman Buhari shiga fadar shugaban kasa bayan sun halarci jana'izar Abba Kyari
An hana wasu manyan hadiman shugaban kasa, Muhammadu Buhari, shiga Villa bayan sun dawo daga jana'izar marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, da aka yi ranar Asabar, kamar yadda SaharaReporter ta rawaito.
Dumbin mutane ne su ka halarci makabartar da aka binne Abba Kyari, yawancin mutanen basu saka takunkumin rufe fuska ko safar hannu ba a matsayin matakin kare yaduwar annobar cutar covid-19.
Akwai fargabar cewa jama'ar sun yi watsi da shawarar NCDC, lamarin da zai iya haifar da yaduwar kwayar cutar covid-19 a makabartar da jama'a su ka yi wa tsinke domin halartar binne marigayi Abba Kyari.
Tun bayan bullar annobar cutar covid-19 a Najeriya aka saka dokokin hana taron jama'a da yawansu ya haura 20 tare da umartar jama'a su zauna a gidajensu don dakile yaduwar cutar.
SaharaReporters ta ce bincikenta ya gano cewa daga cikin hadiman Buhari da aka hana shiga fadar shugaban kasa akwai; Ambasada Lawal Kazaure, Yusuf Sabiu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa.
Sauran sun hada da Musa Haro Daura, dan uwan shugaba Buhari, da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, Babagana Monguno, mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro (NSA), da sauransu.
SaharaReporters ta ce an hana manyan hadiman shiga fadar shugaban kasa ne saboda yadda su ka yi watsi da umarnin nesanta da kare kai daga kamuwa da yada cutar covid-19 yayin jana'izar.
DUBA WANNAN: An sanar da mutuwar mai cutar covid-19 a Kano a karon farko
Gidajen talabijin da dama sun nuna binne gawar Abba Kyari, kuma a wurin ne aka ga manyan jami'an gwamatin da sauran jama'ar da su ka sabawa dokokin da hukuma ta shimfida sakamakon bullar annobar covid-19.
"Jami'an tsaro sun hana duk hadiman shugaba Buhari shiga fadar shugaban kasa bayan dawowarsu daga jana'izar Mallam Kyari, saboda sun yi mu'amala da mutane da yawa, lamarin da ya sabawa umarnin NCDC.
"Shugaba Buhari bai ji dadin yadda hadimansa su ka sabawa umarnin NCDC a kan annobar cutar covid-19 ba, saboda haka ya bayar da umarnin a sanar dasu; su koma su killace kansu," a cewar majiyar SaharaReporters da ke fadar shugaban kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng