An harbi mutum, da dama sun samu rauni yayin zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana fita a Delta

An harbi mutum, da dama sun samu rauni yayin zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana fita a Delta

A kalla mutane uku ne rahotanni suka bayyana cewa an harba tare da raunata wasu ma su yawa yayin zanga - zangar nuna rashin amincewa da kara tsayin dokar kulle da hana zirga - zirga don dakile yaduwar annobar covid-19.

A ranar Laraba ne dumbin mata da matasa su ka mamaye titunan karamar hukumar Sapele domin nuna fushinsu a kan sanarwar karin wa'adin sati biyu don cigaba da zama a gida da gwamnatin jihar ta fitar ranar Talata.

Zanga-zangar, wacce dandazon mata zalla su ka fara a Sapele, ta rikide zuwa hargitsi bayan wasu dumbin matasa sun shiga cikinta, lamarin da ya haifar da rikici da jami'an tsaron da ke aikin tabbatar da biyayya ga dokar zaman gida.

Daily Trust ta rawaito cewa wadanda aka harba; mace daya da maza biyu, na samun kulawa a wani asibiti biyo bayan harbin da ake zargin 'yan bijilanti ne suka yi yayin da al'amura su ka dauki zafi yayin zanga-zangar.

Yayin zanga - zangar, fusattaun matasan sun dinga rera wakar "a bamu abinci, "ba zamu saurari duk wani zance ba".

An harbi mutum uku, da dama sun samu rauni yayin zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana fita a Delta
An harbi mutum, da dama sun samu rauni yayin zanga-zangar rashin amincewa da dokar hana fita a Delta
Asali: Twitter

A ranar Talata ne gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya fitar da sanarwar kara sati biyu a kan dokar hana fita daga gida da taron jama'a biyo bayan karewar wa'adin sati biyun farko da ya ayyana.

Da ya ke rokon jama'a a kan su bi umarnin hukuma da yin biyayya ga dokokin da ta gindaya, Okowa ya ce karin satin biyun za su taimaka wajen zakulo wadanda suka yi mu'amala da mutane uku da aka tabbatar su na dauke da cutar covid-19 a jihar.

DUBA WANNAN: Katsina: An fara bi gida - gida neman wadanda suka dawo daga Abuja da Legas

Kazalika, gwamnan ya bawa jama'ar jihar tabbacin cewa za a raba musu kayan abinci zuwa karshen makon da mu ke ciki.

Amma, fusattatun ma su zanga - zangar sun bayyana cewa mugunta ce ta sa gwamnati ta kara tsawon wa'adin dokar zama a gida bayan ba su da wutar lantarki da abinci a gidajensu.

Masu zanga - zangar da yawancinsu ke sanye cikin jajayen kaya, sun bayyana cewa gwamnati ba ta damu ko yunwa za ta kashesu a gidajensu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel