Ramadan: FG ta bukaci musulmi su cigaba da bin dokokin kare kai daga coronavirus

Ramadan: FG ta bukaci musulmi su cigaba da bin dokokin kare kai daga coronavirus

Gwamnatin tarayya ta gargadi Musulmai a kasar da su guji taron jama’a da kuma tarukan addini a matakin hana yaduwar cutar coronavirus, cewa sai suna raye ne za su ga watan Ramadana.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa a kan COVID-19, Dr Sani Aliyu, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu, a wajen taron kwamitin na 10.

Aliyu ya bukaci Musulmai a fadin kasar da su ci gaba da bin dokar hana zirga-zirga da sauran matakan da gwamnati ta gindaya a lokacin Ramadana.

Ramadan: FG ta bukaci musulmi su cigaba da bin dokokin kare kai daga coronavirus

Ramadan: FG ta bukaci musulmi su cigaba da bin dokokin kare kai daga coronavirus
Source: Facebook

A cewarsa, nisantan mutane na da matukar muhimmanci, sannan kuma cewa akwai bukatar ci gaba da hakan a wannan lokacin.

Kan azumin watan Ramadana mai zuwa da kuma tsoron Musulmai a yanzu da aka tsawaita dokar hana fita a Abuja, Lagas da Ogun, Aliyu ya ce ya zama dole a kare mutane.

Ya jadadda cewa sai mutum na raye ne zai ga Ramadanan wannan shekarar da wasu masu zuwa a gaba.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Ba za mu iya rufe arewa ba - Gwamnoni

A gefe guda, kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.

Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.

Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.

Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.

Haka zalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai cigaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai.

Daga karshe Shehin Malamin ya bayyana dalilin daukan wannan mataki shi ne don dakile yaduwar cutar, don haka ya nemi Musulmai su cigaba da addu’a domin Allah Ya yaye masifar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel