Mayakan Boko Haram sun kashe matafiya 7 a harin kwantan bauna a jahar Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe matafiya 7 a harin kwantan bauna a jahar Borno

Akalla mutane 7 sun gamu da ajalinsu da yammacin Lahadi, 12 yayin da yan ta’addan Boko Haram suka kai harin kwantan bauna a kan wasu motocin haya guda 2 a jahar Borno.

Premium Times ta ruwaito Boko Haram ta tare motocin ne a wajen garin Auno, kimanin kilomita 20 daga garin Maiduguri, a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

KU KARANTA: Annobar Corona: Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada

Mayakan Boko Haram sun kashe matafiya 7 a harin kwantan bauna a jahar Borno
Mayakan Boko Haram sun kashe matafiya 7 a harin kwantan bauna a jahar Borno
Asali: Twitter

A kwanaki ne gwamnatin jahar Borno ta sanya dokar takaita zirga zirga a kan hanyoyin shiga da fita jahar don kare yaduwar Coronavirus, illa babbar hanyar Maidguri zuwa Kano.

Sai dai a halin yanzu, kwamitin ko-ta-kwana a kan COVID-19 dake karkashin Umar Kadafur ta sanar da garkame hanyar ita ma, kuma dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin.

Wani matafiyi dake kan hanyar fita daga Maiduguri da ya yi ido hudu da gawarwakin yace ya kirga gawarwaki guda 7 a Auno, kuma an fada musu a daren jiya aka kai harin.

“Mun wuce wani wuri a Auno da mu ke tunanin Boko Haram ce ta kai hari, daga abin da na gani a wajen, na kirga gawarwakin mutane 7, sai motoci 2 da aka kona; Toyota Hilux da motar kaya dauke da wake.”

Shi ma wani dan yuniyon, Malam Ali ya tabbatar da harin: “Mun samu labarin an kona wata motar daukan kaya a kusa da Auno, amma gaskiya ban san adadin mutanen da aka kashe ba.”

Duk kokarin da aka yin a jin ta bakin Sojoji da Yansanda game da harin ya ci tura, sakamakon kaakakin Soja, Sagir Musa da kaakakin Yansandan jahar Borno, Edet Okon basa daukan waya.

A wani labarin kuma, gungun yan bindiga sun kai munanan hare hare a karshen makon da ta gabata a kauyen Sabon Layin Galadima dake cikin karamar hukumar Faskari ta jahar Katsina.

Da misalin karfe 5 na asuban jiya yan bindiga suka shiga gidan wani manomi, Buhari Umaru, inda suka kashe shi nan take ba tare da daukan komai a gidansa ba.

Ko a ranar Juma’a wasu yan bindiga sun bude ma wata mota wuta a kan hanyar Faskari daga Sabon Layi makare da Fasinjoji da kaya, inda suka kashe karamin yaro, suka jikkata uwarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel