Dokar hana fita: Hankula sun tashi a Legas yayinda yan fashi ke kai farmaki gida-gida

Dokar hana fita: Hankula sun tashi a Legas yayinda yan fashi ke kai farmaki gida-gida

An shiga tashin hankali a yankunan Mangoro, Ogba, Agege, Iyana Ipaja da kuma Dopemu da ke jahar Legas, yayinda yan ta’adda suka yiwa mazauna yankunan fashi da makami.

A wani lamari mai kama da shiryayyen aiki, an tattaro cewa yan fashin sun isa yankunan a kan babura da manyan motocin bas, dauke da makamai daban-daban.

Mazauna yankunan sun bayyana cewa barayin sun sace kayayyakin abinci a shaguna da manyan dakunan ajiya da ke yankunan, jaridar TheCable ta ruwaito.

“Sun zo da misalin karfe 7:00 na dare da babura guda 30 da manyan motocin bas guda 10,” in ji wani mazaunin Aluminium Village a Dopemu.

Dokar hana fita: Hankula sun tashi a Lagas yayinda yan fashi ke kai farmaki gida-gida
Dokar hana fita: Hankula sun tashi a Lagas yayinda yan fashi ke kai farmaki gida-gida
Asali: UGC

“An yiwa gidaje da dama da shagunan siyar da kayan abinci fashi. Sun ma fasa wasu manyan dakunan ajiya sannan suka sace kayayyakin da ke wajen.”

A yankin Mangoro, wani mazaunin wajen ya bayyana cewa mutane na unguwanni, suna yiwa mutane kwace.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus:An sallami 15 amma an samu karin mutane 5 da suka kamu a Najeriya

A Iyana Ipaja, wani mazaunin wajen ya ce bayan hare-haren da aka kai, wasu matasa a yankin sun cinnawa tayoyi wuta a unguwanni.

A wani sako da aka wallafa a soshiyal midiya, wata mazauniyar Agege tace: “A yanzu bamu tsira ba a Agege. Daga Oko koto, Agunbiade, Ayanwale zuwa Pen Cinema. Muna bukatar taimako, mun kira yan sanda amma babu amsa,” in ji ta.

“Kusan awa daya da ya gabata, babu wanda ya kawo mana agaji. Wacce irin kasa ce wannan?

"Sun killace mu ba tare da kowanne tallafi ba. Rayuwarmu na cikin hatsari. Wadannan yaran sun shigo yankinmu. Kusan su 100, Suna ta fashi kusan sama da awa daya.”

Bala Elkana, kakakin yan sandan jahar Legas, ya zargi wadanda suka kona tayoyi da haddasa tashin hankali a yankunan.

“Mun aika jami’anmu wajen, kuma abunda muka lura da matasan shine cewa suna fitowa ne da sunan kare yankunansu daga yan fashi,” in ji shi.

“Sannan suna kona tayoyi da sunan kare kai, alhalin wannan kadai ma yana haifar da tashin hankali. Mun aika wani gagarumin sako, umurnin shine a zauna a gida.

"Dole kowa ya zauna a gida. Muna da isassun jami’an tsaro a wannan lokacin. Bama fuskantar kowani barazana.

"Wadannan matasan na neman damar da zai sa su fito daga gida ne, don haka suke haddasa tashin hankali. Akwai isassun yan sanda da ke sintiri a yankunan.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani sabon rikicin kabilanci ya barke a jahar Taraba tsakanin kabilun Shomo da Jole dake karamar hukumar Lau ta jahar.

Hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Daily Trust ta ruwaito a sanadiyyar rikicin, an kona garin Shomo Sarki gaba daya, inda a nan ne aka fi samun asarar rayuka da dukiyoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng