COVID-19: Gwamnan Bauchi ya halarci sallar Juma'a sa'o'i kadan bayan samun lafiya

COVID-19: Gwamnan Bauchi ya halarci sallar Juma'a sa'o'i kadan bayan samun lafiya

- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a ranar Juma'a ya halarci sallar jami'i

- Hakan ya faru ne bayan sa'o'i kadan da aka sallamo shi daga cibiyar killacewa ta jihar

- Gwamnan ya ki yin hannu da kowa bayan kammala sallar kamar yadda ya saba yi a baya

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a ranar Juma'a ya halarci sallar jami'i.

Hakan ya faru ne bayan sa'o'i kadan da aka sallamo shi daga cibiyar killacewa ta jihar sakamakon warkewa da yayi daga cutar coronavirus.

Gwamnan tare da mataimakinsa, Sanata Baba Tela, kwamishinoni, manyan jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya sun yi jami'i tare da dubban al'ummar Musulmi.

Sallar Juma'ar da aka yi a babban masallacin jihar Bauchin ta zama ta farko da aka ga gwamnan a cikin jama'a tun bayan da aka tabbatar da ya kamu da cutar.

An ganshi sanye da takunkumin fuska da safar hannu a masallacin.

COVID-19: Gwamnan Bauchi ya halarci sallar Juma'a sa'o'i kadan bayan samun lafiya

COVID-19: Gwamnan Bauchi ya halarci sallar Juma'a sa'o'i kadan bayan samun lafiya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Fitattun 'yan Najeriya 6 da suka warke daga COVID-19 (Hotuna)

Sai dai kuma ya ki yin hannu da jama'a kamar yadda ya saba bayan tashi sallar Juma'a din, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An sallama Gwamna Mohammed ne bayan gwaji na biyun da aka yi mishi ya tabbatar da cewa ya warke sarai.

Kwamishinan lafiyan jihar, Dr Aliyu Muhammed Maigoro ya ce an sallami gwamnan ne bayan samfur biyu na jininsa sun nuna ya warke.

"A yau Alhamis ne muke sallamar mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a jihar nan. Ya kasance a cibiyar killacewar na makonni biyu", a cewarsa.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyanawa duniya cewa ya samu waraka daga cutar Coronavirus bayan gwaji na biyu da aka yi masa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita da yammacin Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020.

Yace: "Alhamdulillah. Yanzu na samu labarin. Gwaji na biyu da aka yi mun ya nuna cewa na warke. Ina godiya gareku gaba daya bisa addu'o'inku da goyon baya yayinda nike killace".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel