Shari'a za ta yi iyaka tsakanin Arewa24 da hukumar tace fina-finai
Bayan dakatar da haska shirin Kwana Casa'in da Gidan Badamasi da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano tayi, alamomi na bayyana cewa gidan talabijin din Arewa24 ba zai bi hakan ba.
A jiya ne dai Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma'il Na'Abba Afakalla ta ba gidan talabijin mai zaman kanshi na Arewa 24 umarnin dakatar da haska fina-finan Kwana Casa'in da Gidan Badamasi.
Ta basu wa'adin sa'o'i 48 ne don tabbatar da an dena haska su saboda sun taka dokar jihar Kano.
Kamar yadda wani sashi na takardar da hukumar ta aika wa gidan talabijin din ta bayyana, ta ce ta dauka wannan matakin ne saboda wani sashi na fim din kwana casa'in din ya saba wa al'adar jama'ar jihar Kano.
Akwai wani sashi da aka nuna a shirin makon da ya gabata, inda aka nuna wani mutum ya rungumi wata a cikin wani kantin sayar da kaya na Sahad Stores da ke Kano.
Kamar yadda jaridar Daily Trust Aminiya ta ruwaito, hukumar ta ce tana da alhakin dubawa tare da tantance duk wani fim da aka shirya da Hausa.
A don haka ne take bukatar cewa duk wani fim din na kwana casa'in da za a kara haskawa, sai ta tace.
KU KARANTA: Kano: Hukuma ta haramta nuna fim din kwana casa'in
Kamar yadda masu sani suke zargi, an dakatar da shirye-shiryen ne saboda suna da alaka da siyasa.
Masani kuma mai nazari a fannin fina-finan Hausa, Muhsin Ibrahim, wanda ke koyarwa a kasar Jamus ya ce ba wannan ne karo na farko da ake tuhumar shirye-shiryen da karya doka ba.
Ya ce akwai fitowar da aka cudanya mata da maza a shirin Dadin Kowa, amma hukumar ba tace komai ba saboda shirin bai shafi siyasa kai tsaye ba.
Ya kara da cewa, ya kamata hukumar tace fina-finai ta bi hanyar lalama ne a lamarin, ballantana idan Arewa24 ta ci gaba da nuna shirye-shiryen.
Koda kuwa kotu aka je, akwai yuwuwar Arewa24 tayi nasara kuma a ja musu iyaka da hukumar tace fina-finan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng