Covid-19: NCDC ta karyata batun kashe N1bn don aikewa yan Najeriya da sakonnin waya

Covid-19: NCDC ta karyata batun kashe N1bn don aikewa yan Najeriya da sakonnin waya

- Hukumar NCDC ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa ta kashe naira biliyan daya wajen aikewa yan Najeriya sakonni ta waya

- Hukumar lafiyar ta tarayya ta ce kamfanonin sadarwa ne suka dauki nauyin aikewa yan Najeriya da sakonninta ta waya

- Ya zuwa daren ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu dai, NCDC ta ce mutane 276 ne suka kamu da coronavirus a kasar, yayin da aka sallami mutane 44 bayan sun warke, mutane shida sun mutu

Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta karyata rahotannin da ke ikirarin cewa ta kashe kimanin naira biliyan daya wajen aike wa yan Najeriya sakonnin waya kan yadda za su kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta NCDC ta jadadda cewa ko da yake sadarwa na cikin manyan hanyoyin yaki da annobar covid-19, amma kamfanonin wayar salula ne suka dauki nauyin aike wa da irin wadannan sakonni a matsayin nasu gudunmawar.

Ya zuwa daren ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu dai, NCDC ta ce mutane 276 ne suka kamu da coronavirus a kasar, yayin da aka sallami mutane 44 bayan sun warke, mutane shida sun mutu.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta karbi sawu na 2 na kayan agajin annobar Coronavirus daga China

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar Likitocin Najeriya NMA ta lashi takobin cewa mambobinta Likitoci ba zasu baiwa Likitocin kasar Sin da suka zo Najeriya hadin kai ko kadan ba, Thisday ta ruwaito.

Likitocin sun dira babbar filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ranar Laraba domin taimakawa kasar wajen yakar cutar Coronavirus.

Shugaban kungiyar Likitocin Najeriya NMA, Francis Faduyile, yayinda yayi hira da manema labarai yace akwai sanannen ka'idar da ya kamata duk wani Likita daga kasar waje ya cika kafin iya aikin Likitanci a Najeriya.

Ka'idar itace sai ya rubuta jarabawar majalisar aikin likitanci a Najeriya MDCN kuma ya lashe kafin iya aiki a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bada cewa Likitocin ba aikin likitanci suka zo yi ba, innama sun zo shirya kayayyakin aiki ne da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel