Matasa sun yi zanga-zanga a Kaduna kan kisan wasu mutane 5

Matasa sun yi zanga-zanga a Kaduna kan kisan wasu mutane 5

Matasa a jahar Kaduna sun mamaye unguwanni a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, domin zanga-zanga a kan kisan wasu mutane biyar da ake zargin jami’an yan sanda da yi a garin Trikania da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

An kashe mutanen su biyar ne a wani rikici da ya barke a ranar Litinin, bayan yan sandan da wasu mambobin kungiyar yan bangan JTF sun yi kokarin tarwatsa wasu yan kasuwa.

A cewarsu yan kasuwan sun karya dokar hana fita na jahar, sannan kuma suka turshe yayinda jami'an tsaro ke kokarin tarwatsa su, wanda hakan ne ya yi sanadiyar afkuwar abun bakin cikin.

Yayinda al'umman garin suka fake kan cewa harbin bindigan da yan sandan suka yi ne ya yi sanadiyar mutuwar mutanen, a bangaren yan sanda sun ce lallai basu da hannu a kan kisan.

Matasa sun yi zanga-zanga a Kaduna kan kisan wasu mutane 5

Matasa sun yi zanga-zanga a Kaduna kan kisan wasu mutane 5
Source: UGC

Mutane hudu sun jikkata a rikicin amma suna karkashin kulawar likitoci a yanzu haka.

Tun a ranar 26 ga watan Maris, gwamnatin Kaduna ta tsayar da lamura cak inda ta sanya dokar hana fita na sa'o'i 24 a kokarinta na hana yaduwar cutar COVID-19 a jahar.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnatin Sokoto ta zakulo mutane 26 da suka dawo jahar

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya yi umurnin kama wasu matukan jirgin sama mai saukar ungulu su biyu kan zargin take dokar da gwamnatin jahar ta bayar, domin hana yaduwar annobar coronavirus a jahar.

Kotun majistare na Port Harcourt ta kuma tsare su a gidan yari, yayinda gwamnan ya kaddamar da cewar zai ajiye rigar kariyar da yake da shi a gefe domin shaida a kan duk wanda ya saba dokar rufe iyakar jahar.

Ya bayyana hakan ne a ofishin kwamishinan yan sandan Ribas, Mustapha Dandaura, a Port Harcourt, a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, biyo bayan kama matukan jirgin wanda Wike ya ce sun shiga jahar ba bisa ka’ida ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel