Yayan gwamnan jahar Bauchi ya fito daga hannun masu garkuwa da mutane

Yayan gwamnan jahar Bauchi ya fito daga hannun masu garkuwa da mutane

Yayan gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, watau Yaya Adamu ya kubuta daga hannun miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan kwashe kwanaki 12 a hannunsu.

Jaridar The Nation ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, DSP Kamal Abubakar ne ya bayyana haka ga manema labaru da daddaren Talata, 7 ga watan Afrilu, inda yace:

KU KARANTA: Wata yar Najeriya mai shekaru 64 ta mutu a kasar Ingila sanadiyar cutar Coronavirus

Yayan gwamnan jahar Bauchi ya fito daga hannun masu garkuwa da mutane
Yayan gwamnan jahar Bauchi ya fito daga hannun masu garkuwa da mutane
Asali: Facebook

“Game da tuntubar da kuka yi a kan wannan magana, ina tabbatar muku da cewa wanda aka sacen ya samu yancinsa, kuma a yanzu haka ya koma wajen iyalansa a yau 7 ga watan Afrilu na shekarar 2020.” Inji shi.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun Yansandan bai bayyana ko an biya kudin fansa kafin a sako Yaya Adamu ba, ko kuwa a’a.

Idan za’a tuna ba’a gama jimamin kamuwar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da annobar Coronavirus ba, kwatsam sai aka wasu gungun miyagu yan bindiga suka sace Yayansa, Yaya Adamu.

Yan bindiga sun yi awon gaba da Yaya Adamu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Maris da misalin karfe 7:30 na dare a gidansa dake Unguwan Jaki, cikin kwaryar garin Bauchi.

Wannan lamari ya faru ne bayan kimanin sa’o’i 72 da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa daga cudanya da jama’a sakamakon mu’amalar da ya yi da wani mutumi dake dauke da cutar Coronavirus.

Daga bisani a ranar Talata aka tabbatar da gwamnan ya kamu da cutar, bayan sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, suka gudanar a kansa ya tabbatar da hakan. Babban hadimin gwamnan a kan harkokin watsa labaru, Mukhtar Gidado ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da kama wasu limaman coci coci guda biyu tare da gurfanar da su gaban wata kotun majistri sakamakon kamasu da ta yi da tara gangamin jama’a a cocinsu a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jahar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, inda yace an kama Fastocin ne a unguwar sabon tasha dake cikin karamar hukumar Chikun, inda suke keta umarnin gwamnan jahar na hana duk wasu taruka saboda gudun yaduwar Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel