Farashin diesel da kananzir ya ki sauka duk da karyewar farashin mai

Farashin diesel da kananzir ya ki sauka duk da karyewar farashin mai

Farashin man diesel da na kananzir a Najeriya bai sauka ba har yanzu duk da faduwar farashin danyen man fetir a kasuwar duniya.

Biyo bayan faduwar da farashin mai ya yi, gwamnatin tarayya ta rage farashin kowani litan mai zuwa naira 125 daga naira 145 kan kowani lita a ranar 18 ga watan Maris, 2020.

Hukumar kula da farashin kayan mai ta kuma sanar da farashin litar mai kan N123.59 zuwa N125 a ranar 31 ga watan Maris.

Kafin barkewar annobar Coronavirus wacce ta yi sanadiyar faduwar farashin danyen mai, gwamnatin tarayya na biyan tallafi domin ganin man fetur ya yi araha.

Farashin diesel da kananzir ya ki sauka duk da karyewar farashin mai

Farashin diesel da kananzir ya ki sauka duk da karyewar farashin mai
Source: Depositphotos

Sabanin man fetur, farashin man diesel da kananzir na tafiya ne da karfin kasuwa.

Ana siyar da man Diesel wanda mafi akasarin yan kasuwa ke amfani dashi a janaretonsu a tsakanin N210 da N240 a gidajen mai a Lagas.

An kuma tattaro cewa ana siyar da kananzir wanda mafi akasarin yan Najeriya musamman yan kakkara ke amfani dashi wajen girki a kan N230 kowace lita a Lagas.

Kididdiga daga PPPRA ya nuna cewa tsadar man Diesel ya kasance kan N121.54 kan kowace lita a ranar 6 ga watan Maris yayinda a kasuwa ta ke kan 133.36 kowace lita.

Darakta janar na majalisar kasuwanci na jahar Lagas, Mista Muda Yusuf, ya ce kamata ya yi ace farashin man Diesel da na kananzir ya sauko yanzu duba ga faduwar farashin danyen mai.

Ya ce masu siyar da mai na iya korafin cewa farashin kayayyakin bai sauya ba saboda basu karar da tsoffin kayayyakin da suke dashi ba.

Ya Kara da cewa raunin gashesheniya a kasuwa na iya zama dalilin hakan saboda yawan wadanda ke cikin sana’ar na iya shafar farashin.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Borno ta sake gina gidaje 500 da mayakan Boko Haram suka lalata

Najeriya wacce ta kasance kasar Afrika da ta fi fitar da mai ta dogara ne kacokan a kan man fetur da sauran kayayyakin mai tsawon shekaru da dama.

A wani labari na daban, mun ji cewa Mahmoud Jibril, wanda ya jagoranci gwamnatin tawaren da ta kifar da dadadden shugaban Libya, Muammar Gaddafi a 2011, ya kwanta dama bayan fama da cutar COVID-19.

Aljazeera ta fitar da rahoto cewa Mahmoud Jibril mai shekaru 68 a Duniya ya rasu ne a wani asibitin kasar Masar. Jibril ya yi jinya a asibitin na kusan tsawon makonni biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel