Yunkurin tserewar fursononi: Shugaban kurkukun Kaduna ya 'fede biri har bindi'

Yunkurin tserewar fursononi: Shugaban kurkukun Kaduna ya 'fede biri har bindi'

Sanusi Mu'azu Danmusa, shugaban hukumar gidajen gyaran hali na jihar Kaduna, ya kwatanta rahoton da wasu kafofin yada labarai ke yadawa da labarun kanzon-kurege, wadanda ba alamun gaskiya a cikinsu.

Ya bayyana hakan ne a matsayin martanai a kan rahoton balle gidan gyaran hali na Kaduna da mazauna gidan suka yi yunkurin aikatawa kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A wata takarda da ta fita a ranar Asabar, Danmusa ya ce tabbas wasu daga cikin mazauna gidan sun yi yunkurin balle gidan a ranar 31 ga watan Maris din shekarar 2020.

Shugaban ya bayyana cewa tuni hukumar gidan ta yi bayani a kan aukuwar lamarin amma duk haka ta kara yanke shawarar kara bayani ne don mayar da martani a kan rade-radin da ke yawo a gari.

Yunkurin tserewar fursononi: Shugaban kurkukun Kaduna ya 'fede biri har bindi'

Shugaban gidajen gyaran hali na jihar Kaduna; SM Danmusa
Source: Twitter

Kamar yadda wani sashi na takardar ya bayyana, "Fitar wannan takardar na da matukar amfani. Muna tabbatarwa da jama'a cewa babu abinda hukumar ke son boyewa kamar yadda wasu sashi na kafafen yada labarai ke sanarwa.

DUBA WANNAN: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

"Ballantana an samu asarar rayuwa, mazauna gidan har hudu sun rasa rayukansu a asibiti sakamakon raunikan da suka samu. Hakan ta faru ne sakamakon yunkurin fashe gidan tare da tserewa da suka yi.

Ya kara da cewa, "an fara gamsasshen bincike kamar yadda shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya, Alhaji Jafaru Ahmed, ya bada umarni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel