Yanzu Yanzu: Mutane 8 sun sake kamuwa da coronavirus a Najeriya, sun zama 232

Yanzu Yanzu: Mutane 8 sun sake kamuwa da coronavirus a Najeriya, sun zama 232

- Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bayyana cewa an sake samun karin mutane takwas da suka kamu da cutar COVID-19

- Wadanda suka kamun sun kasance biyar daga Jahar Legas, biyu a Abuja sannan kuma daya a Kaduna

- A yanzu jumullar wadanda suka kamu da cutar sun zama 232, 33 daga cikinsu sun warke, yayinda biyar suka mutu

Rahotanni daga hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ya nuna cewa an sake samun karin mutane takwas da suka kamu da cutar COVID-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

A bisa ga rubutun da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter ta bayyana cewa biyar daga cikinsu suna Jahar Legas, biyu a Abuja sannan kuma daya a Kaduna.

Yanzu Yanzu: Mutane 8 sun sake kamuwa da coronavirus a Najeriya, sun zama 232
Yanzu Yanzu: Mutane 8 sun sake kamuwa da coronavirus a Najeriya, sun zama 232
Asali: Facebook

Jumullar wadanda suka kamu da cutar sun zama 232 kenan, 33 daga cikinsu sun warke, yayinda biyar suka mutu.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama Funke Akindele kan shirya liyafa a gidanta a yayinda aka hana fita

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin jihar Legas a ranar Lahadi ta sanar da cewa an sake sallamar mutane biyar masu cutar Coronavirus bayan samun waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaban jihar.

Gwamnan jihar Legas da kansa, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Lahadi, 5 ga watan Afrilu, 2020.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Legas, a jiya (Asabar) na sanar muku cewa mun sallami mutum daya daga asibitin jinyar cututtuka dake Yaba. A yau Ina farin cikin sanar muku cewa mutane biyar (maza biyu da mata uku) cikin akwai wani dan shekara 10 da haihuwa sun samu waraka daga cutar #COVID19."

"Tuni a mayar da wadannan mutane biyar wajen iyalansu. Yanzu jimillan mutane 29 suka samu waraka tare da sallama a asibitinmu dake Yaba."

"Duk da cewan akwai alamun nasara kan cutar COVID-19, ya kamata mu zange dantse wajen takaita yaduwarta."

Har ila yau mun ji cewa Gwamnatin jihar Osun ta sallami mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus tare da mutane 109 da suka shiga jihar daga kasar Birtaniya da Cote d’Ivoire, bayan an tabbatar basu dauke da cutar.

Gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Abere, Osogbo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel