Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci

Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi jami’an hukumomin tsaro da aka jibge su domin tabbatar da dabbaka dokar hana shige da fice a jahohin Najeriya da su daina cin zarafin jama’a tare da kuntata musu.

Daily Trust ta ruwaito sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na ko-ta-kwana a kan Coronavirus ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabin ayyukansu a ranar Juma’a, a Abuja.

KU KARANTA: Annobar Corona: Dan majalisar Bauchi ya sadaukar da albashinsa N476,000 domin yaki da cutar

Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci
Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci
Asali: UGC

Boss ya yi kira ga yan Najeriya su kasance masu bin doka da oda, tare da kasancewa masu hakuri da kuma kiyayewa. “Sakon shugaban kasa shi ne kada wani dan Najeriya ya cutu a sanadiyyar dokar ta baci da aka sanya.

“Muna samun rahotanni masu faranta rai dake nuna jama’a na bin umarnin zaman gida a Legas, Ogun da babban birnin tarayya Abuja. Cutar COVID-19 fitina ne ga duniya gaba daya, kuma tana barazana ga tsaron kasarmu da tattalin arzikinmu, don haka ya kamata kowa ya taka rawarsa don kawo karshen aikin.

“Ga yan kasuwa maza da mata, muna kira su daina tsawwala farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi, kamata yayi mu kasance masu tausayin juna da sassauci a wannan lokaci, wannan ne lokacin da ya fi kamata mu nuna fahimtar juna.

“Duba da hadarin da ma’aikatan kiwon lafiyanmu suke ciki musamman wadanda ke kula da masu cutar, gwamnati na aiki da masu ruwa da tsaki don samar da inshoran lafiya da inshoran rayuwa gare su, don haka nake basu tabbacin kulawar gwamnati, kuma su masu dage wajen ceton rayukan jama’a.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA, ta bayyana cewa tana tsumayin shigowar wasu manyan jiragen dankaro 27 dake dauke da kayan abinci zuwa cikin gida Najeriya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito hukumar NPA ta bayyana haka ne cikin jaridarta mai suna ‘Shipping Position’ inda tace jiragen zasu fara isowa Najeriya ne daga ranar 3 ga watan Afrilu zuwa 10 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel