Mutumin da ya kamu da cutar Coronavirus ya tofawa wani yawu a fuska kafin ya fadi ya mutu a wajen

Mutumin da ya kamu da cutar Coronavirus ya tofawa wani yawu a fuska kafin ya fadi ya mutu a wajen

- Anan Sahoh dattijo ne mai shekaru 56 wanda ya tofawa wani mutum miyau bayan ya san yana dauke da cutar coronavirus

- Bayan doguwar tafiyar da yayi a jirgin kasa, ya fadi ya mutu a gaban bandakin jirgin kasan bayan ya dinga tari da amai

- Ko kafin shigar shi jirgin, an gwada dumin jikin shi amma daidai yake nunawa, sai dai alamu sun nuna ba shi da lafiya

Wani mutum mai dauke da muguwar cutar coronavirus ya tofa wa wani yawu a fuska yayin da suke hawa jirgi tare a kasar Thailand.

Wani bidiyo wanda na'urar nadar sauti tare da hotuna ta dauka a wani jirgin kasa a Bangkok ya ba mutane mamaki.

A bidiyon, an ga mutum mai fama da cutar coronavirus yana takawa zuwa wurin wani mutum inda ya siya tikiti. A take kuwa ya watsa mishi miyau a fuska.

Mutumin da ya kamu da cutar Coronavirus ya tofawa wani yawu a fuska kafin ya fadi ya mutu a wajen

Mutumin da ya kamu da cutar Coronavirus ya tofawa wani yawu a fuska kafin ya fadi ya mutu a wajen
Source: Facebook

Mai dauke da cutar coronavirus din mai suna Anan Sahoh dan shekaru 56 ne a duniya. Daga karshe kuwa ya mutu a bandakin jirgin kasan wanda ke tafiya zuwa Narathiwat, kamar yadda jaridar Metro UK ta bayyana. Jami'an kiwon lafiya ne suka duba shi inda suka tabbatar da cewa yana dauke da cutar coronavirus.

Sauran fasinjojin sun ce yana tari da amai a jirgin duk da kuwa ya yi gwajin dole kafin shiga jirgin.

A halin yanzu, hukumomi a kasar Thailand na neman mutumin da ya watsa wa yawun a fuska amma har yanzu babu amo balle labarin shi.

Daraktan hukumar jiragen kasa ta Thailand, Thakoon Intrachom, ya ce: "Duk muna cikin damuwa a kan mutumin da aka watsa wa yawu. Da farko dai mun sa 'yan sandan cikin jirgin neman shi amma har yanzu shiru."

KU KARANTA: Tashin hankali: An fara gina makabarta mai girman filin kwallo guda biyu a kasar Ingila saboda mutuwar da mutane suke kan Coronavirus

"Muna sanar da jama'a cewa in har ka san wani ya watsa maka miyau a fuska ko ka ji labarin wanda aka yi wa haka, a gaggauta mika shi asibiti." Ya ce.

Likitoci sun ce Anan Sahoh ya dawo ne daga Pakistan kuma ya mutu ne filin jirgi na Suvarnabhumi. Dukkan binciken da ake yi a wurare, basu bayyana Anan bashi da lafiya ba.

Amma kuma ya fara tari da amai yayin da ake kan hanya. Bayan duba shi da aka yi, sai jami'an kiwon lafiya suka shawarce shi da ya huta a filin jirgin kasa na Hua Hin don dumin jikinshi dai-dai yake, amma sai ya ce yafi so ya ci gaba da tafiyar shi.

Wajen karfe 10:15 na dare ne aka ga gawarshi a kusa da bandakin jirgin kasan bayan an isa yankin Prachup Khiri Khan.

Tuni kuwa aka yi mishi gwaji kuma aka gano yana dauke da muguwar cutar coronavirus da kuma ciwon suga.

Tuni aka kwashe fasinjoji da ke tare da shi da kuma ma'aikatan jirgin biyu, mai gadi da kuma wani dan sanda don killacewa.

Bayan mutuwar Anan, an yi wa jirgin feshi sannan an shawarci sauran fasinjoji da su kauracewa mutane na kwanaki 14.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel