Sudais Ya Magantu da Bama Baman Houthi Suka Kusa Isa Makkah da Madina
- Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, ya yi Allah-wadai da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da ake dangantawa da mayakan Houthi na Yemen
- Al-Sudais ya bayyana cewa kai hare-hare kan wurare mafi tsarki a Musulunci babban laifi ne da bai kamata a lamunta ba, yana mai jaddada cewa za a kare Masallatai Masu Alfarma
- Wannan martani ya zo ne bayan hukumomin Saudiyya sun sanar da kakkabo makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da aka harba zuwa yankuna daban-daban na ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi – Limamin Harami, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya yi Allah-wadai da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da ake zargin mayakan Houthi na Yemen sun kai wa Saudiyya.
Al-Sudais ya bayyana cewa hare-haren sun kasance kai tsaye kan wurare masu tsarki da kuma abin da ke damun Musulmi a faɗin duniya, yana mai jaddada cewa kare Masallatai Masu Alfarma guda biyu wani lamari ne da ba za a yarda a taɓa shi ba.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Al-Sudais ya ce hare-haren da ake ta kai wa sun nuna abin da ya kira mugun nufin mayakan da kuma yadda suke kallon Musulmi da wuraren ibadarsu.
Maganar Sudais kan harin Houthi
Al-Sudais ya bayyana cewa hare-haren sun saɓa wa koyarwar Shari’ar Musulunci wadda ta wajabta kare wurare masu tsarki, da kuma ƙa’idojin jin ƙai na ƙasa da ƙasa.
Ya ce bai kamata a kai hari kan wuraren da Musulmi ke gudanar da ibada ba, yana mai jaddada muhimmancin kare martabar wurare masu tsarki.
Martanin nasa ya biyo bayan wani sabon jerin hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da aka kai wa Saudiyya, inda tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar ya kakkabo makaman da aka harba zuwa yankuna daban-daban.
Inside Haramaini ya wallafa cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Wadi Al-Mughammas a Makkah, unguwar Al-Nuzha a Jeddah, Wadi Jalil a Taif da kuma Masturah a Rabigh.

Kara karanta wannan
Raddin da Jalo Jalingo ya yi wa sarakuna ya sa ya ji babu daɗi hannun ƴan Facebook
An kakkabo makaman Houthi
Hukumomin tsaron Saudiyya sun ci gaba da sanya ido sosai kan sararin samaniyar ƙasar zuwa ranar Lahadi, bayan wasu jiragen sama marasa matuƙa sun nufi yankin Riyadh da sanyin safiya.
Kakakin rundunar haɗin gwiwar da ke yaƙi domin dawo da halastacciyar gwamnati a Yemen, Manjo-Janar Turki Al-Maliki ya ce an kakkabo jiragen saman marasa matuƙan tare da lalata su.
Daga baya, Al-Maliki ya sanar da cewa tsarin kariyar sararin samaniyar rundunar ya kuma kakkabo wani makami mai linzami da aka harba zuwa Riyadh.

Source: Getty Images
Akpabio ya kai mutane Makkah
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce ya shafe shekaru 25 yana taimaka wa Musulmi wajen gudanar da aikin Hajji a Makkah, saboda haka ba zai raina addinin Musulunci ba.
Akpabio ya bayyana hakan ne yayin wani zaman majalisa, inda ya ce a kai a kai yana tura mutane zuwa birni mai tsarki domin yi masa addu’a da Najeriya.
Martanin nasa ya biyo bayan sukar da ya fuskanta sakamakon kalaman da ya yi yayin tattaunawa kan kudirin dokar hana kashe kai na shekarar 2026.
Asali: Legit.ng
