An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin Sojoji da Yansanda a Abuja

An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin Sojoji da Yansanda a Abuja

Yayin da jami’an tsaro suke aikin dabbaka dokar ta baci da gwamnatin tarayya ta sanya a garin Abuja, Legas da Ogun, an samu takaddama a tsakanin wasu dakarun Sojin Najeriya da jami’an Yansanda a unguwar Nyanya na Abuja.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da wasu hafsoshin rundunar Sojan sama guda biyu suka tuka mota ba’a kan hanyarsu ba, har Yansanda suka tare su.

KU KARANTA: Annobar Corona: Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya kyautar Yuro miliyan 5.5

An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin Sojoji da Yansanda a Abuja
An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin Sojoji da Yansanda a Abuja
Asali: Facebook

Tare su ke da wuya sai Yansandan suka nemi su koma baya, su je su bi hanyar da ta kamata, amma Sojojin suka kekashe kasa suka nuna taurin kai tare da dagewa a kan lallai ba zasu koma ba, sai dai Yansandan su basu hanya su wuce.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “Nan take Sojojin suka shiga zagi tare da cin mutuncin Yansandan, har da kwamandansu mai suna Azeez Idowu.” Wannan ne Yasa Yansanda suka yi kokarin kama Sojojin biyu.

Ana cikin wannan takaddama sai kuma ga wasu tawagar Sojojin sama nan sun iso wurin da ake rikicin da nufin kwatar abokan aikinsu ko ta halin kaka, amma Yansandan suka atafau ba zasu kyale su ba.

A nan ma aka cigaba da cacar baki wanda hakan ya janyo zaman dar dar a yankin, da kyar aka shawo kan lamarin bayan wani babban hafsan Sojan sama ya nuna rashin gaskiyar Sojojin, sa’annan ya uamrce su su baiwa Yansandan hakuri.

A wani labarin kuma, babban daraktan hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya bayyana babban kalubalen da suke fuskanta dangane da masu dauke da cutar Coronavirus.

Jaridar Punch ta ruwaito Dakta Chikwe ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, inda yace matsalar da suke fuskanta shi ne yadda zasu killace mutanen da suka dauke da kwayar cutar, amma babu wata alamar cutar a tattare da su.

A cewar Dakta Chikwe: “Idan har mutum ba shi da wata matsala da ido za ta iya gani, amma kuma yana dauke da kwayar cutar, hakan zai sa ba zai iya zama a dakin da muka killace shi ba, don haka muke basu daman yin amfani da wayoyinsu don tuntubar yan uwa da abokan arziki."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel