Likitoci sun ba Abba Kyari gado don ya huta yayinda ya ke samun sauki - Majiya

Likitoci sun ba Abba Kyari gado don ya huta yayinda ya ke samun sauki - Majiya

Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun sauki sosai amma likitocinsa sun nemi ya kara hutawa sosai kamar yadda wasu majiyoyi na kusa dashi suka bayyana, jaridar The Cable ta ruwaito.

Na hannun damar Shugaban kasar ya kamu da cutar Coronavirus a makon da ya gabata amma ya fuskanci alamun ciwon kadan-kadan ne, in ji majiyoyi daga gidansa.

“Tun bayan da ya kwanta, yana dan tari lokaci zuwa lokaci, wanda ya ci gaba koda dai bai jigata shi ba, don haka ya yanke shawarar komawa asibiti mai zaman kansa a Lagas domin cigaba da gwaje-gwaje da kuma kula da yanayin ciwon,” cewar majiyar a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu.

Likitoci sun ba Abba Kyari gado don ya huta yayinda ya ke samun sauki - Majiya
Likitoci sun ba Abba Kyari gado don ya huta yayinda ya ke samun sauki - Majiya
Asali: Twitter

“Har zuwa yanzu, baya jin zazzabi mai zafi kan wahala wajen numfashi, kuma tarin ya fara sauki bayan kulawar likita da yake samu, don haka akwai ci gaba sosai."

Kyari ya shiga killace kansa a ranar 23 ga watan Maris bayan gwajin.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Sakamakon gwajin mutane 22 cikin 25 da ake zargin sun kamu a Kano ya fito

A wani labarin kuma mun ji cewa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya yi martani a kan jita-jitar da ake yadawa na cewa shugaba Buhari ya sallami shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin tarayya, Abba Kyari.

Wata wasikar sallama daga aiki na ta yawo a yanar gizo a ranar Laraba wacce ke bayyana korar Kyari daga aiki.

Amma kuma sakataren gwamnatin tarayya ya ce wasikar ta bogi ce. A kusan makonni biyu da suka gabata ne aka gano cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasan na dauke da muguwar cutar coronavirus.

A halin yanzu kuwa abu mai wahala ne a ce ga inda yake duk da cewa ya ce zai garzaya jihar Legas don killace kansa tare da karbar magunguna. S

akataren gwamnatin tarayya, wanda ya yi martanin ta daraktan yada labarai na ofishin gwamnatin tarayyar, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa wannan rahoton ba gaskiya bane kuma ayi watsi da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel