Jiragen yaki sun yi luguden wuta a babbar mafakar 'yan Boko Haram a Sambisa

Jiragen yaki sun yi luguden wuta a babbar mafakar 'yan Boko Haram a Sambisa

Jiragen yaki na rundunar sojin sama ta Najeriya a karkashin atisayen 'Operation Lafiya Dole' sun yi luguden wuta tare da baje daya daga cikin manyan mafakar mayakan kungiyar Boko Haram da ke Parisu a cikin dajin Sambisa.

Luguden wutar ya yi sanadiyar mutuwar dumbin mayakan kungiyar Boko Haram tare da lalata dukkan sansanin.

A cikin jawabin da darektan yada labaran atisayen rundunar soji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya fitar ya ce rundunar soji za ta cigaba da rike wuta a yakin da take yi da 'yan ta'adda.

"Daya daga cikin manyan hare-hare na kwanan baya bayan nan da rundunar soji ta kai a kan 'yan Boko Haram, shine na maboyarsu da ke Parisu a cikin dajin Sambisa a ranar 31 ga watan Maris. Na'urorin cikin jirgi yaki masu ido sun hango maboyar 'yan Boko Haram da motsinsu a wurin.

"Jiragen yaki sun yi luguden wuta a sansanin, lamarin da ya yi sanadiyar dumbin mayakan Boko Haram tare da baje mafakar tasu," a cewar jawabin.

Jiragen yaki sun yi luguden wuta a babbar mafakar 'yan Boko Haram a Sambisa
Jirgin yakin NAF
Asali: Facebook

A ranar Laraba ne, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa dakarun sojin kasar Chad harin kwanton bauna a cikin makon da ya gabata, dakarun sojojin kasar ta Chadi sun kai wa mayakan kungiyar harin ramuwar gayya a cikin satin da muke ciki.

A yayin da yake ganawa da kwamandojin rundunar sojojin hadin gwuiwa (MNJTF) a Baga ta jihar Borno bayan harin daka kai wa sojojin kasarsa, shugaban kasar Chadi, Idriss Derby, ya bawa sojojin umarnin su fara wani atisaye, ba tare da nuna tausayi ba, a yankin tafkin tekun Chadi.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu, an ga sojojin kasar Chadi suna wakokin karawa junansu karfin gwuiwa yayin da suke harbawa mayakan kungiyar Boko Haram makami mai nisan zango (RPG) a lokacin da suke kazamar musayar wuta.

DUBA KARASHEN LABARIN: Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel