Ka dakatar da karbar kudin wuta da ruwa na tsawon wata biyu - Dan majalisar wakilai Shehu Koko ya roki shugaba Buhari

Ka dakatar da karbar kudin wuta da ruwa na tsawon wata biyu - Dan majalisar wakilai Shehu Koko ya roki shugaba Buhari

- Wani dan majalisar wakilai, Shehu Koko yayi kira ga shugaba Buhari a kan ya daukewa jama'a kudin wuta da na ruwa na watanni biyu

- Dan majalisar wakilan na tarayya ya bayyana cewa hakan zai matukar zama tallafi ga jama'a a wannan lokacin tsananin da 'yan kasa ke ciki

- Dan majalisar mai wakiltar Maiyama/Koko/Besse a tarayya ya ce duk da wadannan ababen more rayuwar ba na gwamnati bane, zai fi kyau idan aka daukewa 'yan kasa

Wani dan majalisar wakilai, Shehu Koko, yayi kira ga shugaba Buhari a kan ya bada umarnin dakatar da karban kudin wuta da na ruwa daga 'yan Najeriya na watanni biyu a matsayin hanyar sassauci garesu, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Koko mai wakiltar mazabar Maiyama/Koko/ Besse a tarayya karkashin jam'iyyar APC yayi kiran ne a takardar da ya saki a ranar Litinin.

KU KARANTA: Dokar hana zirga-zirga a Kaduna: 'Yan sanda sun kama mutane 165 sun kuma kwace ababen hawa 205

Wani bangaren tarkardar yace, "A halin yanzu kasar mu na cikin jarabawa kamar yadda sauran kasashen duniya suke ciki. A yayin da muke ci gaba da addu'a ga Ubangiji, ina kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ababen more rayuwa da suka hada da wutar lantarki da ruwan sha a kyauta.

"Na yarda hakan zai matukar taimako ga jama'a wajen sassauci a kan annobar da ta barke. Duk da wadannan ababen more rayuwar nan ba na gwamnati bane, muna kira ga gwamnati da ta taimaka don sassautawa jama'a," takardar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel