Coronavirus: Ku cika gidajenku da kayan abinci – Minista ga mata

Coronavirus: Ku cika gidajenku da kayan abinci – Minista ga mata

- Pauline Tallen, Ministar harkokin mata, ta bukaci yan Najeriya da su dauki matakan kare kai sannan su cika gidajensu da kayan abinci

- Ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da gwamnati ta yi umurni ga al'umman kasar kan cewa su zauna a gida domin hana yaduwar annobar coronavirus

- Ta roki kungiyoyin mata da su mutunta hukumomin da aka kafa sannan su bi dukkanin umurnin gwamnati kan kauracewa taron jama’a

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta bukaci yan Najeriya da su dauki matakan kare kai sannan su cika gidajensu da kayan abinci domin su kasance a gida a kokarin rage yaduwar cutar annobar coronavirus.

Da take jawabi ga manema labarai a Abuja kan coronavirus, ministar ta bukaci mata da su bi doka domin hana yaduwar annobar a kasar.

Coronavirus: Ku cika gidajenku da kayan abinci – Minista ga mata
Coronavirus: Ku cika gidajenku da kayan abinci – Minista ga mata
Asali: UGC

Ta roki kungiyoyin mata da su mutunta hukumomin da aka kafa sannan su bi dukkanin umurnin gwamnati kan kauracewa taron jama’a kamar tarukan kauye, tarukan birane, bukukuwa, taron mutuwa da dukkanin tarurruka a wannan lokaci da ake ciki.

Idan za ku tuna a baya mun kawo maku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a birnin tarayya Abuja, da kuma jihohin Ogun da Legas, na tsawon makonni biyu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan ne a jawabin da ya yiwa yan Najerya da yammacin Lahadi, 29 ga Maris, 2020.

A cewarsa, dukkan mazaunan wadannan jihohi su kasance cikin gidajensu kuma su guji tafiya zuwa wata jiha.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Ba mutanen da ya kamata ayi wa gwaji muke yiwa ba – Gwamnan Niger

Amma ya togaciye wani bangaren mutane da ya hada da yan kasuwa masu sayar da kayan abinci, kamfanonin man fetur, ma-aikatan wutan lantarki da jamian tsaro masu zaman kansu.

Hakazalika kamfanonin sadarwa, da kuma yan jaridan da ba zasu iya aiki daga gida ba.

Yace “Bisa ga shawarar maaikatar kiwon lafiya da hukumar NCDC, ina bada umurnin hana hada-hada a Legas da birnin tarayya na tsawon kwanaki 14 fari daga karfe 11 na dare na ranar Litinin, 30th ga Maris, 2020.“

“Wannan dokar hana fitar za ta shafi jihar Ogun saboda kusancinta da jihar Legas da yawan tafiye-tafiyen da ake tsakaninsu.“

“Lallai mun san wannan mataki zai tsanantawa mutane da dama, amma wannan lamarin rayuwa ko mutuwa ne idan muka lura da irin yadda ake mutuwa kullum a Italiya, Faransa da Andalus.“

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel