Dangote zai samar da cibiya mai gado 600 don killace masu coronavirus a Kano
Hamshakin attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, zai samar da wata cibiyar killace wa mai gado 600 domin duba wadanda suka kamu da kwayar cutar coronvirus a jihar Kano.
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da kwamitin neman kudin taimakawa masu karamin karfi a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wani gajeren sako da Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren sabbin kafafen sadarwa, ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta a ranar Lahadi.
A daya daga cikin labarab da Legit.ng ta wallafa a yau, Lahadi, attajirin dan kasuwar da kansa ya sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar COVID-19.
An ji tsoton cewa Dangote zai iya kamuwa da kwayar cutar coronavirus bayan ya yi mu'amala da Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka tabbatar da cewa yana dauke da kwayar cutar.
DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta ankarar da jama'a a kan sabon salon damfara da sunan COVID-19
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Dangote ya bayyana cewa ya yi gwajin ne a matsayinsa na dan kasashe da dama sannan shugaba a kasuwanci.
Ya ce yana jagorantar shugabannin a bangaren kasuwanci domin taimakon gwamnati a kokarinta na dakile yaduwar cutar.
Dangote ya bayyana cewar annobar cutar coronavirus ta taba lafiyar jama'a da sauran harkokinsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng