Likafa ta cigaba: Buhari ya amince da nadin yan Najeriya 16 a matsayin sabbin manyan sakatarori

Likafa ta cigaba: Buhari ya amince da nadin yan Najeriya 16 a matsayin sabbin manyan sakatarori

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin yan Najeriya 16 a matsayin sabbin manyan sakatarorin ma’aikatu daban daban, kamar yadda ofishin shugabar ma’aikatar Najeriya ta bayyana.

Punch ta ruwaito shugaba Buhari ya amince da nadin ne a ranar Talata, 25 ga watan Maris, kamar yadda daraktan watsa labaru na ofishin shugabar ma’aikatan Najeriya, Folashade Yemi, Esan, watau Olawunmi Ogunmosunle ta bayyana.

KU KARANTA: Yanzun nan: An sanar da sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi ma gwamnan Nassarawa

Daraktan ta ce sabbin manyan sakatarorin za su maye guraben manyan sakatarorin da za su yi murabus a shekarar 2020 ne, daga cikin wadanda za su yi murabus akwai manyan sakatarori daga jahohin Kwara, Kebbi, Abia, Anambra, Cross River, Kaduna, Kano, Oyo, Rivers, Sokoto, Adamawa, Yobe, Gombe da Jigawa.

Haka zalika sanarwar ta bayyana cewa shugaban kasa ya amince da cike guraben manyan sakatarori daga jahohin Zamfara da Kogi, wanda hakan ya kawo adadin sabbin sakatarorin da za’a nada zuwa 16.

Sanarwar ta cigaba da fadin shugaban kasa ya bada umarnin a fara zaben daraktocin da za su maye guraben daraktocin da zasu samu karin girma zuwa mukamin manyan sakatarori, sa’annan shugaban kasan ya amince da sauya ma manyan sakatarori uku wurin aiki.

Sakatarorin da aka sauya ma ma’aikatu sun hada da An dauke da babban sakataren fadar shugaban kasa Jalal Arabi zuwa ma’aikatar jin kai da kula da yan gudun hijira, babban sakataren ma’aikatar jin kai da kula da yan gudun hijira, Tijjani Umar zuwa fadar shugaban kasa.

Sai kuma babban sakataren ma’aikatar sufuri, Sabiu Zakaro zuwa ma’aikatar tsaro. Daga karshe sanarwar ta bukaci manyan sakatarorin da su koma bakin aiki a sabbin ma’aikatun nan take.

A wani labarin kuma, wannan shi ne rana zafi inuwa kuna, ba’a gama jimamin kamuwar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da annobar Coronavirus ba, kwatsam sai ga wasu gungun miyagu yan bindiga sun sace Yayansa, Yaya Adamu.

Yan bindiga sun yi awon gaba da Yaya Adamu ne a ranar Laraba, 25 g watan Maris da misalin karfe 7:30 na dare a gidansa dake Unguwan Jaki, cikin kwaryar garin Bauchi.

Wannan lamari ya faru ne bayan kimanin sa’o’i 72 da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa daga cudanya da jama’a sakamakon mu’amalar da ya yi da wani mutumi dake dauke da cutar Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel