COVID-19: An haramtawa adaidaita sahu daukar fasinjoji, an saka wa masu mota sabuwar doka a Kaduna

COVID-19: An haramtawa adaidaita sahu daukar fasinjoji, an saka wa masu mota sabuwar doka a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramtawa babura masu kafa uku da aka fi sani da 'adaidaita sahu' da kananan motocin haya (taxi) jigilar mutane saboda basu cika ka'idar nesanta da ake bukata ba a yayin da ake fama da annobar cutar coronavirus.

Da take sanar da hakan a ranar Laraba, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, an dauki wannan sabon matakin ne yayin wani taro da manyan jami'an gwamnatin jihar suka gudanar domin tattauna wa a kan matakan da aka dauka na dakile yaduwar kwayar cutar COVID-19.

Dakta Hadiza ta ce, ya zuwa yanzu ba a hana manyan motocin haya (bus) daukar fasinjoji ba, amma ba a yarda su dauki sama da mutum biyu ba a layin kujera daya ba a cikin motocinsu.

A cewarta, gwamnatin jihar a shirye take ta dakatar da duk wani nau'in sufuri a motocin haya idan yanayi ya nuna da akwai bukatar yin hakan.

A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta dauki babban mataki domin kare yaduwar annobar kwayar cutar coronavirus bayan ta umarci dukkan ma'aikatanta daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida na tsawon kwanaki 30 masu zuwa.

COVID-19: An haramtawa adaidaita sahu daukar fasinjoji, an saka wa masu mota sabuwar doka a Kaduna
Dakta Hadiza da El-Rufa'i
Asali: Twitter

Kazalika, gwamnatin ta umarci duk wasu 'yan kasuwa su rufe shagunansu. Masu shagon sayar da magani da kayan abinci kadai aka yarda su bude shagunansu a jihar.

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnan Bauchi ya aike sako ga jama'ar jiharsa bayan tabbacin yana da cutar

A cikin jerin wasu sakonni da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da jami'an tsaro wajen tabbatar da cewa an yi wa dokar hana jama'a da yawa taruwa a wuri guda biyayya, musamman a coci-coci, masallatai da kuma makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da ma na addini.

Gwamnan ya shawarci jama'a da su zauna a gidajensu tare da gujewa fitowa waje matukar hakan ba dole ya zama ba, saboda halin da ake ciki na fama da annobar kwayar cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel