Buhari ya bayyana takaicin mutuwar Sojojin Najeriya 50 a hannun Boko Haram

Buhari ya bayyana takaicin mutuwar Sojojin Najeriya 50 a hannun Boko Haram

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa bisa kisan zaratan dakarun Sojojin Najeriya fiye da 70 da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka yi a jahar Borno a ranar Asabar din da ta gabata.

Sahara Reporters ta ruwaito mayakan Boko Haram sun kai ma Sojojin Najeriya harin kwantan bauna ne a kauyen Gorgi dake jahar Borno inda suka kashe jami’an rundunar da dama.

KU KARANTA: Yadda babbar kasuwar Kaduna ta koma bayan dokar El-Rufai a kan Coronavirus

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka inda yace Buhari ya jajanta ma iyalan Sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu ga kasa Najeriya. “Sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba.”

Buhari ya ce mutuwar kowanne Sojan Najeriya na masa zafi, saboda yawan ciwon dake tattare da zama Soja, sa’annan yana sane da hadarin da suke shiga a sakamakon aikinsu, don haka ya yi kira ga Sojojin Najeriya gaba daya da kada su bari wannan ya kashe musu gwiwa.

A hannu guda kuma rundunar Sojan kasa ta aika da sabbin dakarunta zuwa kauyen domin dauko mata rahoton yadda harin ya kasance tare da duk wasu bayanai da ta ke bukata don kauce ma sake aukuwar hakan a gaba.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan jahar Zamfara ta sanar dakama wani kasurgumin dan bindiga mai suna Sani Boka dake kauyen Masama cikin karamar hukumar Gummi na jahar Zamfara bayan ya kashe surukinsa, sa’anann ya sace ya yi garkuwa da kanwarsa.

Kwamishinan Yansandan jahar, Usman Nagogo ne ya bayyana haka yayin da yake holen mutumin, a babban ofishin Yansandan jahar, wanda da kansa ya bayyana ma yan jaridu laifin da ya aikata.

A cewar Nagogo, kanwarce ta gane fuskar Sani Boka a lokacin da suka kai musu farmaki, kuma ta shaida ma Yansanda cewa yana daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ita tare da abokiyar zamanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng