Annobar Corona: Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutun dole

Annobar Corona: Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutun dole

A kokarin ta na dakatar da yaduwar mugunyar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus, gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatanta hutun dole, inda ta nemi su yi aikin da za su iya yi daga gida.

Jaridar TheCable ta ruwaito shugabar ma’aikatan Najeriya, Yemi Esan ce ta bayyana a ranar Litinin, 23 ga watan Maris cikin wata sanarwa da ta aika ma dukkanin ma’aikatun gwamnati.

KU KARANTA: Annobar Corona: Bankin Access ta garkame ofishinta a Legas bayan bullar cutar

Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin jami’an gwamnatin tarayya daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida ba sai sun fita ofis domin aiki ba, haka zalika wadanda kuma lallai sai sun tafi wajen aiki toh su rage adadin bakin da ke kai musu ziyara.

“Kamar yadda kuka sani ne, gwamnatin tarayya ta dauki matakai daban daban domin zakulo masu dauke da cutar COVID-19 tare da dakatar da yaduwar ta, don haka gwamnati ta damu da walwalar dukkanin ma’aikata, kamar yadda ta damu da walwalar yan Najeriya.

“Shi yasa ta umarci duk ma’aikata su dabbaka umarnin gwamnati da shawarwarin da take bayarwa game da yaki da annobar don kare yaduwar ta, da wannan ne muke umartar ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su yi zamansu a gida daga ranar Talata 24 ga watan Maris, har sai yadda hali ya yiwu.” Inji ta.

A wani labarin kuma, masana kiwon lafiya a kasar Birtaniya, kwararru a sashin Kunne, Hanci da Makogwaro sun gano wasu sabbin alamomin cutar Coronavirus, daga ciki akwai daina jin dandano a harce da kuma daina gane kamshi ko wari.

Kungiyar likitocin Kunne, Hanci da Makogwaro na kasar Ingila ne suka sanar da haka, inda suka ce wadannan alamomi suna bayyana ne a inda sanannun alamomin cutar basu bayyana a jikin mai dauke da kwayar cutar ba.

Don haka suka ce duk mara lafiyan dake fama da wadannan matsaloli biyu, akwai yiwuwar yana dauke da cutar Coronavirus, saboda an samu ire iren mutanen nan a kasashen China da Kudancin Koriya, inda suka kira alamomin ‘Anosmia.’

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel