Hotuna: Alaka mai karfin gaske na kulluwa tsakanin Rahama Sadau da Adam A Zango

Hotuna: Alaka mai karfin gaske na kulluwa tsakanin Rahama Sadau da Adam A Zango

- Hankalin mutane ya karkata kan wasu hotuna da suka fita a makon nan na jaruma Rahama Sadau da Adam A Zango

- Hotunan dai sun nuna yadda jaruman suka dauki hoton cikin nishadi da yanayi na shakuwa

- Hakan ya sanya mutane suke ganin ko dai jaruman sun fara soyayyane ya sanya suke irin wannan hotuna

A rayuwa komai yana iya sauyawa abinda kake tsoro ka iya baka tausayi wata rana abinda ke baka tausayi ka iya baka tsoro, haka masoyi kan zama makiyi kamar yadda makiyi kan rikide ya zama masoyi, hakan ya sanya ake mana gargadi da zafafa soyayya da kuma zafafa kiyayya komai dai ayi shi sama-sama.

Idan baku manta ba shekaru uku zuwa hudu da suka gabata an samu rashin jituwa tsakanin jarumi Adam A Zango da jaruma Rahama Sadau, inda yayi yunkurin sakata a fim din sa mai suna 'Duniya Makaranta' jarumar tayi wani furuci da ya sanya Zango cire ta daga fim din, inda wannan dalili ya haddasa rashin jituwa tsakanin sa da ita har matsalar ta shafi Ali Nuhu, inda aka zarge shi da ganin Rahama tana yiwa Zango rashin kunya bai tsawatar mata ba magana dai ta dinga girma a lokacin.

KU KARANTA: N300 yake bani don ciyar da yara 8 - Matar aure ta sanar da kotu

Daga baya aka yi sulhu tsakaninsu, inda sulhun tsakanin Rahama da Zango ya dore, amma tsakanin Zango da Ali Nuhu abin bai yiwu ba, duk kuwa da cewa sun danganta sabanin nasu da rigingimun da yaransu ke haddasawa, amma su suna kaunar juna kamar yadda Ali Nuhu ya bayyana a hirar da yayi da BBC Hausa, haka zalika Zango yayi bayani makamancin haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arewa24.

Sai dai a 'yan kwanakin nan wata alak mai karfi da ake gani tana kulluwa tsakanin Rahama Sadau da Adam A Zango ta fara bawa mutane da dama mamaki duba da yadda suke yawan hotuna tare cikin nishadi wanda har wani sa'in hotunan kan kawo kace-nace.

Hotuna: Alaka mai karfin gaske na kulluwa tsakanin Rahama Sadau da Adam A Zango
Hotuna: Alaka mai karfin gaske na kulluwa tsakanin Rahama Sadau da Adam A Zango
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel