Nan bada jimawa ba za mu fara daukan sabbin Yansanda 10,000 – Minista

Nan bada jimawa ba za mu fara daukan sabbin Yansanda 10,000 – Minista

Ministan kula da al’amuran Yansandan Najeriya, Muhammad Dingyadi ya bayyana cewa nan bada jimawa ba hukumar Yansanda za ta fara daukan sabbin kuratan Yansanda 10,000 a duk fadin Najeriya.

Punch ta ruwaito hakan na daga cikin cika alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na samar da sabbin jami’an Yansanda 40,000 a tsawon shekaru hudu na wa’adin mulkinsa.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Dingyadi ya bayyana cewa sun fara tsara yadda daukan aikin zai kasance, wanda suke sa ran zai kara adadin jami’an Yansandan Najeriya tare da taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Minista Dingyadi ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin bikin kaddamar da littafi mai suna; “Introduction to law enforcement: A training guide for the Nigeria Police Force.’ Wanda AIG Adeyemi Ogunjemilusi mai ritaya ya wallafa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda 10,000 da gwamnatin tarayya ta dauka a shekarar da ta gabata suna cigaba da samun horo a yanzu haka a kwalejojin horas da Yansanda dake fadin kasar nan.

“A yanzu nan da nake magana, muna cigaba da horas da matasa 10,000 da muka dauka aikin Dansanda a shekarar da ta gabata, kuma kamar yadda shugaban kasa ya umarta, mun fara shirin daukan sabbin Yansanda 10,000.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hukumar bautan kasa ta Najeriya, NYSC, ta garkame dukkanin sansanonin horas da yan bautan kasa dake fadin Najeriya a wani mataki na gaggawa don gudun yaduwar annobar cutar Coronavirus a tsakanin matasan.

Rukunin farko na yan bautan kasan sun fara samun horo a sansanonin NYSC dake fadin jahohin Najeriya ne a ranar 10 ga watan Maris, kuma kamata yayi su kwashe kwanaki 21 a sansanonin, amma sai ga shi bayan kwanaki 8 an sallame su.

Da dama daga cikin matasa masu yi ma kasa hidima sun shiga rudani yayin da a tsakar daren Talata aka sanar dasu cewa an kawo karshen horaswan da zasu samu a sansanonin, don haka aka mika ma kowannensu takardar aikin da zai yi, da kuma inda aka tura shi aikin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel