Asirin wani dalibi dake sayar ma yan bindiga wiwi da miyagun kwayoyi a Zamfara ta cika

Asirin wani dalibi dake sayar ma yan bindiga wiwi da miyagun kwayoyi a Zamfara ta cika

Wani dalibin jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau, Mansur Mohammed ya shiga hannun jami’an Yansandan Najeriya reshen jahar Zamfara bisa zarginsa da ake yi da sayar ma yan bindiga tabar wiwi da miyagun kwayoyi.

Jaridar Punch ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Usman Nagogo ne ya bayyana haka yayin da yake holensa ga manema labaru, inda yace Mansur dalibi ne dan aji uku a jami’ar Gusau, kuma sun kama shi ne bayan samun bayanan sirri a kansa.

KU KARANTA: Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

“A tsawon lokaci, wannan matashi ne shi ne yake yi ma kungiyoyin miyagun yan bindiga safarar tabar wiwi da miyagun kwayoyi, wanda hakan ke kara rura matsalar hare haren yan bindiga a jahar Zamfara.” Inji shi.

Daga cikin kayan shaye shayen da aka gano daga wajen Mansur akwai Codeine kwalabe 59, kati 20 na kwayar rohypnol da kuma kunshi guda biyu na tabar wiwi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin al’adun gargajiya na kamun kifi da noma da aka gudanar a garin Argungu na jahar Kebbi karo na farko bayan kwashe tsawon shekaru 11 ba tare da an yi shi ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya bayyana dawowar bikin a matsayin wata manuniya dake nuni ga nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro a Najeriya.

Buhari ya nanata manufar gwamnatinsa na cigaba da inganta harkar tsaro domin habbaka bukukuwan al’adu da yawon bude ido, tare da janyo masu zuba hannu jari a bangaren nishadantarwa na Najeriya.

“Halartarmu yau a bikin baje kolin amfanin noma a garin Argungu tabbaci ne na manufarmu na inganta tsaro tare da fadada hanyoyin samar da abinci a cikin gida, muna sane da cewa an dakatar da wannan biki na shekara shekara tsawon shekaru 11 saboda matsalar tsaro.

“Amma cikin ikon Allah a yau bikin ya dawo, kuma ina fatan ya dawo da alheri, baya ga murnar dawowar wannan biki, muna farin cikin cigaba da aka samu a fannin samar da tsaro a yankin nan, ina kara sanar daku cewa an fara gasar tseren motoci daga Abuja zuwa Argungu a ranar Laraba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel