Rundunar 'yan sanda ta kama wasu kansilolin Zamfara da laifin garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sanda ta kama wasu kansilolin Zamfara da laifin garkuwa da mutane

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Usman Nagogo, ya tabbatar da kama wasu kansilolin jihar Zamfara bisa zarginsu da hannu a sace wasu kansiloli 4 a karamar hukumar Gummi a ranar 4 ga watan Maris.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da sace kansilolin a makon jiya. Kansilolin da aka sace sune kamar haka; Murtala Arzika na mazabar Gayari, Lawal AC Milan na mazabar Ubandoma da Sahabi Abubakar na mazabar Birnin Tudu. An sace su ne a hanyarsu ta zuwa Gusau daga Gummi.

Da yake holin masu laifi a hedikwatar rundunar 'yan sadan jihar Zamfara da ke Gusau, kwamishina Nagogo ya bayyana cewa har yanzu rundunar 'yan sanda na gudanar da bincike a kan batun sace kansilolin.

"Da farko ban so yin magana a kan yin garkuwa da kansilolin ba saboda har yanzu muna gudanar da bincike a kan maganar.

Rundunar 'yan sanda ta kama wasu kansilolin Zamfara da laifin garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sanda ta kama wasu kansilolin Zamfara da laifin garkuwa da mutane
Asali: UGC

"Mun gano cewa akwai siyasa a cikin lamarin, musamman idan aka yi la'akari da yadda aka sace su.

DUBA WANNAN: Sarautar gargajiya: Sheikh Ahmad Gumi ya yi 'ragargaza' bayan an tsige Sanusi II

"Akwai fasinja guda daya da ya sauka daga motar a hanya bayan an umarci dukkan na cikin motar a kan kar su sanar da kowa, hatta iyalansu, a kan inda zasu je," a cewar Nagogo.

Da yake amsa tambaya a kan rahoton cewa daya daga cikin kansiloli ya samu kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane, sai Nagogo ya bayyana cewa hakan na daga cikin abubuwan da suke bincike saboda kansilan ya gudu, har yanzu kuma basu san inda yake ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel