Da sauran tsalle: Hukumar yaki da cin hanci a Kano za ta cigaba da tuhumar Sanusi II

Da sauran tsalle: Hukumar yaki da cin hanci a Kano za ta cigaba da tuhumar Sanusi II

- Hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bincike a kan tubabben sarkin Kano

- Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta hana hukumar bincikar tubabben sarkin a kan zarginsa da ake da damfara

- Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Rimingado ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya Talata, cewa ana ci gaba da bincike

Hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bincike a kan tubabben sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, bayan umarni daga kotu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta hana hukumar bincikar tubabben sarkin a kan zarginsa da ake da damfarar naira biliyan 2.2.

Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Rimingado ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya Talata, cewa ana ci gaba da bincike.

"Ko a ranar Litinin hukumar ta gayyaci wasu kamfanoni kuma duk sun zo. Amma kuma za a ci gaba da bincikar tubabben sarkin bayan umarni daga kotu," Rimingado yace.

Da sauran tsalle: Hukumar yaki da cin hanci a Kano za ta cigaba da tuhumar Sanusi II
Da sauran tsalle: Hukumar yaki da cin hanci a Kano za ta cigaba da tuhumar Sanusi II
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sheikh Ahmad Gumi ya yi 'ragargaza' a kan tsige Sanusi II

Yace tube sarkin zai sa hukumar ta samu damar yin bincike ba tare da wani katsalandan ba ko wani shinge.

"A halin yanzu muna da sararin bincike tunda babu sarkin a kusa," ya kara da cewa.

Idan zamu tuna, a ranar Alhamis 5 ga watan Maris ne hukumar ta amince da dage bayyanar sarkin a gabanta har zuwa ranar 9 ga watan Maris.

Amma kuma, basaraken wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne, a ranar Juma'a 6 ga watan Maris, ya mika korafi a gaban kotu a kan hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel