"Daurin talalar da aka yi wa Muhammadu Sanusi II ya ci karo da doka da hakkin ‘Dan Adam"

"Daurin talalar da aka yi wa Muhammadu Sanusi II ya ci karo da doka da hakkin ‘Dan Adam"

Kungiyoyi masu rajin kare hakki da nemawa Bil Adama ‘yanci sun fara magana game da gudun hijirar da aka tura tsohon Sarkin Birnin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

Wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa tsare tsohon Sarkin da aka yi a wani Kauye a jihar Nasarawa ya sabawa dokokin Najeriya, sannan kuma an keta masa hakkinsa.

Kungiyar Amnesty International ta na cikin ‘yan gaba-gaba wajen wannan kira. Darektan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho ya fitar da jawabi na musamman a Ranar Talata.

Osai Ojigho ya bukaci hukumomin Najeriya su saki tsohon Mai martaba Muhammadu Sanusi II. A cewarsu, tsare shi da hana sa magana ya ci karo da dokokin gida da kuma na waje.

Haka zalika kungiyoyi irinsu CISLAC sun nuna damuwarsu game da yadda ake ta tsare tsohon Sarkin Birnin bayan an tube masa rawanin gidan dabo a cikin farkon makon nan.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta yi magana bayan tunbuke Sarkin Birnin Kano

Darektan kungiyar CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana cewa maida tsohon Sarkin zuwa Nasarawa da karfi da yaji ya ci karo da sashe na 34, 35, 36, 40 da 41 na tsarin mulki.

Shugaban kungiyar nan ta Concerned Nigerians, Deji Adeyanju, ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran hukumomi wasika game da tsare tsohon Sarkin.

A takardar da Deji Adeyanju ya aikawa Jami’an tsaron Najeriya da ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja, ya ce tura Sanusi II gudun hijira ya sabawa doka da tsarin mulkin kasa.

SERAP ta ja hankalin majalisar dinkin Duniya game da halin da tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya ya ke ciki. Alamu na nuna cewa za a kai kara kotu idan ba a sake shi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel