Muhammadu Sunusi mai murabus ya koma kauyen Loko a jahar Nassarawa

Muhammadu Sunusi mai murabus ya koma kauyen Loko a jahar Nassarawa

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus ya tattara inasa inasa ya koma kauyen Loko dake cikin karamar hukumar Nassarawa ta jahar Nassarawa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito tsohon Sarkin ya samu rakiyar hadimansa da wasu jami’an gwamnatin jahar Kano inda suka sauka a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe da yammacin Litinin, 9 ga watan Maris.

KU KARANTA: Iyayi: Ku daina mana ta’aziyya, ba mutuwa aka mana ba – diyar Malam Muhammadu Sunusi II R

Daga nan kuma suka nufi sabon gidansa dake kauyen Loko a cikin ayarin motoci tare da jami’an tsaro, inda ne za’a masa daurin talala, babu shiga babu fita.

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sanar da tsige Muhammadu Sunusi a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatin jahar Alhaji Usman Alhaji.

Gwamnatin ta bayar da hujjojinta guda uku wanda ta bayyana su ne suka sabbaba gwamnan daukan mataki mai tsauri a kan Sarkin da suka hada da rashin da’a, kin halartar zaman tattaunawa da kuma karya dokokin masarautar Kano, kamar yadda sakataren gwamnatin jahar Kano ya bayyana.

Sai dai tuni gwamnatin ta sanar da tsohon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano, yayin da dan uwansa Nasiru Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Bichi.

Nadin Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano ya samu amincewar manyan fadawan masarautar Kano guda hudu wadanda suka isa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Litinin domin tattaunawa da Gwamna Ganduje kafin sanar da sunan sabon Sarkin Kano.

Manyan masu nadin Sarkin sun hada da Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Abdullahi, Sarkin Dawaki Mai Tuta Abubakar Tuta da Sarkin Bai Mukhtar Adnan.

A wani labarin kuma, biyo bayan tsige tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus, diyarsa ta fito a kafar sadarwar zamani ta Twitter tana yin gargadi tare da kashedi ga masu jajanta musu.

Diyar Malam Sunusi mai murabus, Yusrah Sunusi ta yi kira ga abokan huldarta a kafar sadarwar zamani ta Twitter da cewa su daina jajanta musu saboda ba mutuwa aka musu ba, kuma basu mutu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel