Zaratan matasa yan sa kai sun kubutar da mutum 2 daga hannun yan bindiga a Katsina

Zaratan matasa yan sa kai sun kubutar da mutum 2 daga hannun yan bindiga a Katsina

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Yakasai dake cikin karamar hukumar Kurfi ta jahar Katsina, inda suka yi awon gaba da mutane uku a daren Lahadi, 8 ga watan Maris.

Jaridar daily trust ta ruwaito daga cikin mutanen da yan bindigan suka tafi dasu akwai wani dattijo mai suna Audu Haruna, da wani matashi mai suna Sabe da kuma wata guda daya.

KU KARANTA: Harin ta’addanci a Masallaci ya jikkata Musulmi 1 a kasar Faransa

Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga garin da tsakar dare, inda kai tsaye suka zarce gidan Malam Haruna, suna ta harbe harben mai kan uwa da wabi, a haka suka yi awon gaba da mutanen uku.

Sai dai cikin ikon Allah, wasu zaratan matasa yan sa kai sun kalubalanci yan bindigan bayan sun ji abin da ke faruwa, inda suka fuskancesu aka yi ta dauki ba dadi har sai da suka kwato matar da yan bindigan suka sace da matashi Sabe.

Kwamandan yan sa kai na Kurfi, Nura Liman ya bayyana cewa: “Da tsakar dare ne yan bindigan suka kai hari, inda suka harbi Sabe a kafa, sa’annan suka daki Harisu a kai, sai kuma suka dauke Sabe da wata mata.

“Ba tare da bata lokaci ba jama’an kauyen suka fada mana halin da ake ciki, nan da nan muka bazama inda muka ci karo da barayi guda 6, kuma muka kwato Sabe da matar, amma sun tafi da Haruna, amma sun harbi abokin aikinmu daya, Murtala Dan Bauchi, kuma yana samun lafiya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Katsina ta samu nasarar damke wuyar wani gawurtaccen barawon mutane da ya shahara wajen sata tare da garkuwa da mutane a jahar Katsina da kewaye.

Kakakin Yansandan jahar, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace Yansanda sun kama mutumin ne a ranar 7 ga watan Maris.

SP Gambo ya bayyana sunansa kasurgumin barawon a matsayin Kabiru Lawal dan shekara 30 mazaunin Ruwan Godiya a jahar Katsina, inda yace sun kama shi ne da misalin karfe 11:30 na dare.

Kaakakin yace asirin Kabiru ya tonu ne a daidai lokacin da shi tare da sauran miyagun abokansa suka kai farmaki gidan wani mutumi Alhaji Nasiru Ibrahim dake Rugar Kadi, a kauyen Ruwar Godiya a karamar hukumar Faskari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel