Mun kashe mayakan Boko Haram 19 a Damboa, sun kashe Sojoji 3 – rundunar Soji

Mun kashe mayakan Boko Haram 19 a Damboa, sun kashe Sojoji 3 – rundunar Soji

Hukumar rundunar Sojin kasa ta Najeriya ta sanar da mutuwar dakarunta guda 3 a yayin harin da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai garin Damboa a ranar Laraba, 4 ga watan Maris.

Daily Trust ta ruwaito jami’in Soja mai magana da yawun Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda yace baya ga Sojoji da suka mutu, guda hudu sun samu rauni.

KU KARANTA: Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya

Sai dai Kanal Aminu ya ce Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram guda 19 yayin da wasu da dama suka samu munana rauni, sa’annan sun kwace bindigu biyar kirar AK-47 da sauran kayan aikin yan ta’addan.

Aminu ya bayyana cewa yan ta’adda a kan motoci da dama tare da wasu mayakansu a kasa sun yi kokarin afka ma garin Damboa ta bangarori uku, amma Sojoji ba su yi wata wata ba mayar da martani, yayin da Sojoji sama suka dinga sauke musu ruwan wuta.

A cewar Aminu, wannan na daga cikin manyan shan kayi da Boko Haram ta taba fuskanta a hannun Sojojin Najeriya tun shiga sabuwar shekarar 2020.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jinjina tare da yaba ma dakarun Sojojin Najeriya na Operation lafiya Dole bisa jarumtar da suka nuna a yayin artabun da suka yi mayakan Boko Haram a Damboa a ranar Laraba.

Zulum ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace ba zai iya jurewa ba har sai ya bayyana ma duniya yadda Sojojin Najeriya na sama da na kasa suka yi ma yan Boko Haram rakiyar kura tare da tafka musu mummunan asara.

“Da misalin karfe 6 na safiyar Laraba yan Boko Haram suka kaddamar da hari a garin Damboa ta bangarori daban daban da nufin afka ma garin, sai dai sun ci karo da zaratan Sojoji dake cikin shirin yaki a kullum, nan da dakarun kasa da na sama suka shiga artabu dasu.

“A hannu guda Sojojin sa kai na Civilian JTF da yan banga suna taimaka musu, nan take suka lalata motocin Boko Haram 13, tare da kashe duk wadanda suke ciki. Amma abin da ya fi burgeni shi ne bayan yan ta’addan sun tsere, Sojoji basu tsaya ba, sai suka bi su a guje har sai da suka sake lalata motocinsu guda 6, tare da kashe karin yan ta’adda da dama.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel