Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa

Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa

Al'ummar anguwan Ja'en da ke karamar hukumar Gwale ta jihar Kano ta tsame kanta daga cikin masu korafi ga majalisar jihar Kano a kan ta binciki Sarki Muhammadu Sanusi II a kan zargin karantsaye ga al'adun gargajiyar jihar Kano.

Anguwan Ja'en karkashin shugabannin anguwar a wata takardar hadin guiwa da Kwamared Tameem Bala Ja'en da Kwamared Ibrahim Yahya Ja'en suka sa hannu bayan wani taro. Sun bukaci majalisar jihar Kano da ta fito da wanda yayi korafin saboda anguwar ba ta san me wannan sunan ba.

Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa
Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sanatan APC ya yi Alla wadai da mulkin dimokradiyya, ya yabi mulkin soji

Idan zamu tuna, a ranar 4 ga watan Maris ne majalisar jihar Kano din ga kafa kwamitin mutane 8 da zasu binciki Sarki Sanusi a kan korafin da wani Mukhtar Muhammad Ja'en ya mika gareta wanda yake zargin Sarkin da yin karantsaye ga al'adun gargajiyar jihar Kano.

Kamar yadda takardar ta ce, anguwar ta tsame kanta daga wannan korafin kuma tana jaddada biyayyarta da mubaya'a ga Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

Anguwar ta kara da barazanar daukar matakin shari'a a kan majalisar jihar matukar suka kasa samar da Mukhtar Muhammad Ja'en, wanda ya kaiwa korafin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel