Magidanci ya kashe kansa da kansa bayan ya gano matarsa tana neman maza

Magidanci ya kashe kansa da kansa bayan ya gano matarsa tana neman maza

Wani magidanci dan shekara 48 mai suna Felix Edore ya halaka kansa ta hanyar kwankwadar kwalar fiya fiya biyo kama matarsa da ya yi da laifin cin amanarsa ta hanyar neman maza duk kuwa da cewa igiyar aurensu na daure.

Jaridar Punch ta ruwaito Felix ya yanke ma kansa wannan danyen hukunci ne sakamakon bacin rai da ya shiga a sanadiyyar bankado asirin matarsa wanda suka kwashe shekaru 16 suna tare, ashe a bayan idon sa tana neman maza.

KU KARANTA: Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

Majiyarmu ta ruwaito Felix yana sana’ar tuka motar Tasi ne daga Abraka-Etsu zuwa Sapele a jahar Delta, ya kwankwadi fiya fiya ne a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Sapele, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti, a washegarin Asabari ya mutu, kamar yadda likitoci suka tabbatar.

Makwabtansu sun bayyana Felix a matsayin mutumin kirki wanda yake jin dadin sana’ar da yake yi, kuma bai dade da sayen motar da yake amfani da ita ba.

Ita ma wata makwabciyarsu mai suna Mama Rita ta bayyana cewa: “Felix ya kashe kansa ne bayan ya tabbatar da zargin da yake ma matarsa na neman maza, yaransu 6, kuma ya dade yana korafi kan halinta na neman maza, sau da yawa sun sha rikici a kan maganan, inda aka saba jiyo shi yana barazanar kashe kansa saboda ita.

“A wannan rana bamu san ya sayo fiya fiya ba, ko kafin mu ankara har ya kwankwadi abinsa tun a cikin mota, daga nan ne jama’a suka hange shi, suka mika shi zuwa asibiti, inda a can ya mutu.” Inji ta.

A wani labarin kuma, kwana dubu na barawo, kwana daya rak na mai kaya kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa ya sanar da kama wasu miyagun mutane masu sata tare da garkuwa da jama’an da basu ji ba, basu gani ba.

Kwamishina Inuwa ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Warri inda yace Yansanda sun kama barayin ne a tsakanin ranakun Lahadi da Litinin a Oghara, karamar hukumar Ethiope ta yamma.

A cewar kwamishinan, mutane hudu daga cikinsu sun amsa laifin satar wata mata mai suna Victoria Okereka daga asibitinta a ranar 22 ga watan Feburairu, wanda suka saketa bayan ta kwashe kwana guda a hannunsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel