Hukumar hisbah ta damke almajirai 21 a Kano

Hukumar hisbah ta damke almajirai 21 a Kano

Rahotanni sun kawo cewa hukumar Hisbah ta jahar Kano ta tabbatar da kama almajirai guda 21 a yammacin ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairu.

Babban Daraktan hukumar, Dr. Aliyu Musa ya ce kamen almajiran da suka yi na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan Kano Abdulllahi Umar Ganduje ya bayar na kama yaran da ke bara tare da iyayyensu ko masu kula da su.

Ya ce suna kamen almajirai tun baya da aka kafa dokar hana bara a jihar cikin 2014, amma dai a nan gaba za su fadada wannan aiki zuwa kan iyayen wadanda suka kama.

Hukumar hisbah ta damke almajirai 21 a Kano
Hukumar hisbah ta damke almajirai 21 a Kano
Asali: Twitter

Gwamna Ganduje dai a ranar Talata ya bada umarni, a cikin tsarin hade almajirai da kuma karatun dole na firamare da na sakandare na jahar, cewa kada a kara ganin wani almajiri yana bara a jahar.

Sai dai kuma mun ji a baya cewa Babbar Kungiyar koli ta addinin Musulunci a jihar Kano, ta soki hukuncin gwamnatin jihar na haramta bara a kan titunan jihar da ta yi. Ta ce hakan bai dace ba kuma gwamnatin jihar ba ta dau lamarin ta yadda ya dace ba.

Kungiyar malaman jahar Kano din karkashin shugabancin Sheikh Ibrahim Khaleel, ta bayyana cewa wannan matakin ba shi ya dace gwamnatin ta dauka ba.

Ya jaddada cewa akwai bukatar a tantance wanne irin bara ce aka haramta kuma a saka duk masu ruwa da tsaki a harkar kafin a kaddamar da ita.

Ya ce, “Don haramcin yayi aiki, akwai bukatar hadin kai tsakanin gwamnati da malaman tsangaya. Akwai bukatar tattaunawa, a gano kiyasin yawan yaran, dalilin hana bara da kuma sanin mutane nawa za a shigar. Akwai bukatar hada kai da wasu jihohi masu makwabtaka da jihar in har ana bukatar tabbatar lamarin.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun kwanaki 2 kafin yi masa gwaji

Sheikh Khaleel ya yi kira ga gwamnatin da ta tuntubi duk masu ruwa da tsaki da kuma malamai don samar da mafita mai dorewa wajen kashe bara kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel