Buhari ya bayyana abubuwan da za su sa ya bude iyakokin Najeriya

Buhari ya bayyana abubuwan da za su sa ya bude iyakokin Najeriya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada sharadin bude iyakokin kasar nan don barin kaya su shigo daga kasashe masu makwabtaka. Ya bayyana cewa bude iyakokin kasar nan ya dogara ne a kan rahoton kwamitin bangaroti uku da ya kafa tare da gwamnatocin Najeriya, jamhuriyar Benin da jamhuriyar Nijar.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a lokacin da ya hadu da Shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore na kasar Burkina Faso, wanda ya kai masa ziyara a ranar Juma'a a gidan gwamnati da ke Abuja, kamar yadda Channels TV suka ruwaito.

"Babbar matsalarmu shine tsaro, shigo da makamai, harsasai da kuma kwayoyi," ya ce kamar yadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya sanar.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara da cewa, "mun fahimci raguwa a ta'addanci tun bayan da muka rufe iyakokin kasarmu. Hakazalika, manonanmu yanzu na iya siyar da shinkafar gida tunda mun dena shigo da ta Turai wacce ke cika kasar nan."

Ya sanar da bakonsa cewa Najeriya ta yanke hukuncin sakaya iyakokinta ne saboda tabbatar da tsaron kasa.

Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar nan
Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar nan
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ba mu maraba da kai a jam'iyyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP

"Zanyi aiki da gaggawa matukar na samu rahoto," Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tabbatar wa da Kabore.

Shugaban Burkina Faso din shine shugaban kwamitin ECOWAS wanda hakkin shawo kan matsalar rufe iyakoki ya rataya wuyansu.

Ya sanar da shugaban kasar Najeriya din cewa ya zo ziyarar ne don sauke hakkin ECOWAS da ke kansa.

Shugaban kasa Kabore ya ce, akwai kalubale da yawa wadanda suka sa Najeriya ta garkame iyakokinta wadanda shugaban Najeriya ya sanar masa. Yayi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da ya kara duba matsayarsa.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya halarci taron, ya bayyanawa manema labaran gidan gwannati abinda aka tattauna.

Ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya damu da damuwar kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya ballantana idan ya duba yarjejeniyar sahale kai kawo tsakanin kasashen ECOWAS din.

Onyeama yayi bayanin cewa an rufe iyakokin kasar nan ne saboda dalilan tsaro, duk da ya ce akwai fatan budesu nan ba da dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel