Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya

Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya

- To dai ance soyayya gamon jini, domin kuwa wasu na shan bakar wahala wajen rabuwa da masoyi

- Sai dai labarin Mr Le Van ya wuce gona da iri, inda shi soyayyar tasu har tsoka ta taba

- Domin kuwa bayan mutuwar matarshi Mr Le Van yaje har makabarta ya tono gawarta ya dawo da ita gida yana kwana da ita na tsawon shekaru 16

Mutane da yawa suna matukar shiga damuwa idan suka rasa masoyi, wani mutumi dan kasar Vietnam, ya tono gawar matarshi ya sanya ta a cikin gunki yake kwanciya da ita a gado daya na tsawon shekaru 16.

A lokacin da labarin Mr Le Van ya bazu a shekarar 2009, mutane da yawa sun dauka kage ake yi masa, da yawa sunki yadda da cewa mutum zai iya zuwa ya tono gawar matarshi daga makabarta, ya kawo ta gida ya kuma dinga kwanciya da ita a gado daya.

Sai dai wannan shine abinda Mr Le Van ya dinga yi na tsawon shekaru 16, duk kuwa da irin sukar da yake samu daga wajen 'yan uwanshi da abokan arziki na kauyensu, mutumin bai da niyyar mayar da ita kabari.

Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya
Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya
Asali: Facebook

Mr Van da matarshi sunyi aure a shekarar 1975. Lokacin basu ma san junansu ba ballantana ayi zancen soyayya, iyayensu ne kawai suka hada su aure tun suna yara. Bayan auren sai soyayya ta shiga tsakaninsu, suke zamansu cikin jin dadi da soyayya.

Sun haifi yara bakwai, sai dai wata rana a shekarar 2003, lokacin Mr Van yana wurin aiki kawai sai labari yaji cewa matarshi ta rasu. Cikin gaggawa ya nufi gida, yana zuwa yaga fuskar matar nashi na dan lokaci sai aka binne ta.

KU KARANTA:

Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya
Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya
Asali: Facebook

Da farko, Mr Van ya koma rayuwa a cikin makabarta ne kusa da kabarin matarshi, inda yake kwana a wajen. Amma daga baya sai sauyin yanayi ya fara damunshi, irinsu sanyi da zafi. Sai ya yanke shawarar tono gawar matar tashi domin ya kaita gida ya cigaba da kwanciya da ita. Ba a jima ba 'ya'yanshi suka gano cewa yana kwana a makabarta, kuma suka hana shi kwana a ciki. Duk da haka ya kasa daina tunanin matar tashi.

Bayan 'ya'yanshi sun gano abinda yayi, sai suka fusata suka bukaci ya mayar da gawar mahaifiyarsu cikin kabarinta, amma yaki, yace musu ba zai iya rayuwa ba idan babu ita. Makwabta sun daina zuwa gidanshi bayan sun gano cewa ya kawo kasusuwan matarshi cikin gidanshi yana kwana da ita. Wasu ma har sun sanar da jami'an tsaro cewa Le Van zai kawo cuta garin. 'Yan sanda sunyi kokarin rarrashin shi akan ya mayar da ita, amma mutumin nan yaki yadda, sai suka hakura.

Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya
Ya shafe shekara 16 yana kwanciya da gawar matarsa a daki daya
Asali: Facebook

"Lokacin da matata ke da rai, bata sanya kaya masu kyau sosai, yanzu dole na nema mata kaya masu kyau. Ina canja mata kaya sau biyu kullum," Le Van ya ce. "Mutane na cewa na haukace saboda ina kula da gawa, amma ni na san cewa koda yaushe tana tare dani. Zan cigaba da kwanciya da gawarta har lokacin da zan bar duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel