Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci

Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci

Wani dan Najeriya mai suna Malam Ibrahim Ibrahim da ke fuskantar hukuncin kisa a kasar Saudi Arabia a kan safarar miyagun kwayoyi ya samu 'yancinsa. Malam Ibrahim dan asalin jihar Zamfara ne kuma ya kai shekaru uku a garkame bayan an kama miyagun kwayoyi a cikin kayansa.

Duk da wasu kananan kotu uku a kasar Saudi Arabia sun wanke malamin dan asalin jihar Zamfara, amma hukumomi a kasar Saudi sun daukaka kara wanda a yau Talata aka saurari shari'ar.

Wani lauya dan Najeriya wanda yake cikin wakilan da suka tafi jiya Litinin zuwa kasar ne ya sanar da jaridar Solacebase sakin Malam Ibrahim Ibrahim jim kadan bayan zaman kotun.

Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci
Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci
Asali: Twitter

Idan zamu tuna. a yau ne Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ya tura wakilai zuwa kasar Saudi Arabia don ceto rayuwar dan asalin jihar Zamfaran da ke fuskantar hukuncin kisa a kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa wakilan gwamnatin sun hada da kungiyar lauyoyi a cikinsu. Wannan na kunshe ne a wata takarda da Zailani Bappa, mai bada shawara na musamman ga gwamnan a kan yada labarai, ya mika ga manema Labarai a garin Gusau a ranar Litinin.

Amma kuma gwamnan ya samu shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da bukatar gwamnatin tarayya ta sa hannu wajen kokarin wanke Ibrahim tare da tseratar da ransa. Tuni dai shugaban kasa ya umarci ministan shari'a Abubakar Malami, da ya shiga maganar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel