Kwace kujerar APC a Bayelsa: Atiku ya yi martani

Kwace kujerar APC a Bayelsa: Atiku ya yi martani

Dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019,Alhaji Atiku Abubakar ya nuna jin dadin shi da kuma gamsuwa da hukuncin kotun koli a zaben jihar Bayelsa, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Idan zamu tuna, hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana David Lyon a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Bayelsa din a zaben da aka yi a watan Nuwamba na 2019.

Amma kuma a ranar Alhamis, alkalan kotun kolin da suka samu jagorancin Mai shari’a Mary Odili sun umarci INEC da ta janye shahadar zama gwamnan daga Lyon din jam’iyyar APC. Sun umarceta da ta mika shahadar ga jam’iyyar da ke da kuri’u mafi yawa na biyu.

Kotun kolin tayi haka ne don jaddada hukuncin babbar kotun tarayya da ta bayyana rashin dacewar takarar abokin tafiyar Lyon din. Ta zargesa da mikawa INEC shaidar takardun makaranta na bogi yayin tantancewa.

A yayin martani ga wannan hukuncin, Atiku yayi wallafa a shafinsa na tuwita inda ya nuna jin dadinsa a kan hukuncin kotun kolin.

Kwace kujerar APC a Bayelsa: Atiku ya yi martani
Kwace kujerar APC a Bayelsa: Atiku ya yi martani
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Ya yi kira ga jama’ar jihar Bayelsa da su hada kansu wajen mayar da jihar Bayelsa ‘Aljannar duniya’.

Ya kara kira ga kotun kolin da ta cigaba da jajircewa wajen zartar da hukuncin tare da kawo mafita ga ‘yan Najeriya ba tare da duban wanda abin zai shafa ba.

Kamar yadda ya wallafa, “Na samu labarin hukuncin kotun koli inda ta bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa din. Nayi matukar farin ciki da jin cewa Sanata Duoye Diri ne halastaccen gwamnan jihar Bayelsa.”

Ina kira ga jama’ar jihar Bayelsa da su zauna lafiya tare da rungumar junansu don mayar da jiharsu ‘Aljannar duniya’. Daga karshe ina kira ga kotun kolin da ta ci gaba da jajircewa wajen zartar da hukunci tare da kawo mafita ga ‘yan Najeriya ba tare da duban wanda abin zai shafa ba.” Ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel