Yanzu-yanzu: Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan APC David Lyon, ta bawa PDP

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan APC David Lyon, ta bawa PDP

-A yau Alhamis ne kotun koli ta kwace kujerar zababben gwamnan jihar Bayelsa na jam'iyyar APC, David Lyon

- Kotun kolin ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta kwace shahadar da ta ba Lyon da mataimakinsa

- Wannan na zuwa ne ana sauran kwanaki kadan a rantsar da David Lyon tare da Biobarakuma Degi-Eremienyo

A yau Alhamis ne kotun koli ta kwace kujerrar zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon da kuma abokin tafiyarsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, wadanda suke ta shirye-shiryen karbar rantsuwar hayewa karagar mulkin jihar.

Alkalai biyar na kotun, wadanda suka samu shugabancin Mai shari'a Mary Peter-Odili, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta janye shahadar hayewa kujerar jagorancin jihar da ta mikawa 'yan takarar jam'iyyar APC din a jihar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Kotun kolin ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta mika shahadar ga jam'iyya mai biye da ta APC din a yawan kuri'u a jihar idan aka duba sakamakon zaben da aka yi a ranar a 2019.

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan APC David Lyon, ta bawa PDP
Yanzu-yanzu: Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan APC David Lyon, ta bawa PDP
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari

Duba da wannan kalami kuwa, jam'iyyar PDP ce za ta amshe wannan kujerar don ci gaba da mulkin jihar ta Bayelsa.

Mai shari'a Ejembi Ekwo, wanda ya karanto hukuncin kotun kolin, ya bada wannan umarnin ne bayan da aka bayyana rashin cancantar mataimakin David Lyon, Degi-Eremienyo a tsayawa takarar zaben.

Kotun ta jaddada hukuncin ranar 12 ga watan Nuwamba na 2019 wanda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na rashin cancantar abokin takarar Lyon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel