Allah Sarki: Bidiyon yadda wani mutumi ya fashe da kuka bayan matarshi ta gudu wajen sabon saurayinta ta bar shi da yara miskinai guda 4

Allah Sarki: Bidiyon yadda wani mutumi ya fashe da kuka bayan matarshi ta gudu wajen sabon saurayinta ta bar shi da yara miskinai guda 4

- Wani bidiyon dattijo yana zubda hawaye bayan matar shi ta tsere don komawa wajen wani dan majalisa ya yadu

- Kamar yadda bidiyon ya nuna, dattijon na zubda hawaye ne tare da kokarin tattara yaransu hudu masu nakasa da matar shi ta bar mishi

- Abinda har yanzu ba a gano ba shine sunan dan majalisar da kuma matar da ta bar yaranta hudu masu lalura ta bi shi

Abin tausayi ne kuma a zubda hawaye. Bidiyon wani tsoho ne wanda yake zubar da hawaye bayan matar shi wacce suka haifa yara hudu ta gudu ta bar shi.

Kamar yadda ya bayyana daga bidiyon, mahaifiyar yaran shi hudu ta gudu ne don komawa hannun wani da majalisa.

Duk da ba a bayyana inda wannan lamarain ya faru ba, jaridar Pulse Ng ta ruwaito ne bayan da Adom TV suka wallafa bidiyon.

Dattijon cike da kunar rai yake kukan takaici, bakin ciki da kuma bacin rai yayin da yake ta kokarin daukar yaran hudu masu nakasa.

KU KARANTA: Hotuna: Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja

Abinda ba a kuma bayyana a bidiyon ba shine sunan dan majalisar da kuma sunan matar tashi da ta bar yaranta nakasassu har hudu don son abin duniya.

Duk da sau da yawa an san mata da tausayi tare da son yaransu, wasu kuwa na da karfin hali wanda matukar son abin duniya ne ke kawo shi.

Ba wannan ne karo na farko da aka taba jin mace ta bar talaka komai kuwa matsananciyar soyayyar da suke ba, ta koma wajen mai hannu da shuni don ganin ita kanta ta huta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel