Wuta mai ban mamaki ta kama gidan Obasanjo, ta tafka mummunan barna

Wuta mai ban mamaki ta kama gidan Obasanjo, ta tafka mummunan barna

An shiga cikin tashin hankali da dimuwa yayin da wata mummunan gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.

Jaridar The Nation ta ruwaito gobarar ta tashi ne a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu, da misalin karfe 9:30 a gidan dake unguwar Ita-Eko dake cikin garin Abekuta, sai dai shaidun gani da ido sun bayyana cewa lantarki ne ya janyo gobarar.

KU KARANTA: A shirye nake na sadaukar da rai na domin kawo zaman lafiya a Arewa maso gabas – Dan majalisa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da kyar da sudin goshi makwabta da ma’aikatan gidan suka samu nasarar kashe wutar bayan sun mata taron dangi bayan sun kwashe kimanin awa daya suna fama da ita.

Shaidun sun bayyana cewa wutar ta yi ta tashi daga wani sashi zuwa wani sashin gidan saboda iskar bazara.

Sai dai daraktan hukumar kashe gobara na jahar Ogun, Fatai Adefala ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace wutar ta cinye iyakar wani dakin ajiyan kaya ne, ba wai asalin gidan ba. Sa’annan yace jami’an hukumarsu sun kashe wutar da kayan aikinsu.

A wani labarin kuma, hukumar majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwarta game da yiwuwar kungiyar ta’adda ta kaddamar da harin ta’addanci a majalisa, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ya bayyana.

Wannan jami’I da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Da gaske ne, mun samu mummunan rahoton tsaro dake bayyana cewa majalisar dokokin Najeriya na daga cikin wuraren da yan ta’adda ke shirin kaddamar da hari, kuma ba na wasa bane.”

Jami’in yace suna yawan samun bakin fuskoki dake shiga cikin majalisa a yan kwanakin nan, kuma hakan ya zama abin damuwa ga hukumar majalisar, kamar yadda ya shaida.

Jami’in ya kara da cewa a lokutta da dama da zarar jami’an hukumar ko jami’an tsaro sun tunkari wadannan bakin fuskoki game da dalilin zuwansu majalisar sai su ce sun zo wurin wakilansu ne, bugu da kari jami’an tsaron majalisar sun yi karanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel